Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani Game da Adaora Umeoji, Shugabar Bankin Zenith
- Kasa da wata daya kenan da aka nada Adaora Umeoji a matsayin babbar darakta ko kuma ace babbar shugabar bankin Zenith
- Ta kasance tare da bankin sama da shekaru 20, ta yi aiki a fannonin gudanarwa daban-daban na sama da shekaru goma
- Nasarar Umeoji wani abin zaburarwa ne ga ƙwararrun ƴan matan Najeriya da dama da ke neman yin zarra a fannoni daba-daban na rayuwa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kasa da wata daya kenan da nada Adaora Umeoji a matsayin babbar shugabar bankin Zenith (GMD/CEO), wadda babban bankin Najeriya (CBN) ya amince da ita.
An bayyana nadin nata ne a cikin wata sanarwa da bankin ya fitar ga Nigerian Exchange Limited (NGX) a ranar Talata, 19 ga Maris, 2024.
Umeoji ta karbi mulki daga hannun Dr. Ebenezer Onyeagwu, wanda wa'adinsa zai kare a ranar 31 ga Mayu, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za ta karbi sabon matsayinta a matsayin GMD/CEO a watan Yuni 2024.
Abubuwan sani game da Adaora Umeoji
Ilimi
A cewar sanarwar da bankin Zenith, Umeoji ta yi digirin farko a fannin zamantakewar al’umma daga Jami’ar Jos, digiri na farko a fannin Accounting da kuma digiri na farko a fannin shari’a daga Jami’ar Baze Abuja.
Ta yi digirinta na biyu a fannin shari'a a Jami'ar Salford, Birtaniya tare da samun digirin digirgir kan harkokin kasuwanci daga jami'ar Calabar.
Ita tsohuwar daliba ce ta makarantar kasuwanci ta Harvard kuma ta halarci makarantar kasuwanci ta Wharton, a shirin tunani da gudanarwa na Amurka.
Umeoji tana da shaida a fannin tattalin arziki na kasuwanci daga babbar makarantar MIT Management Sloan da kuma shedar ilimin Jagoran Kasuwancin Duniya daga makarantar kasuwancin Harvard, Amurka.
Tana daya daga cikin manyan ma'aikatan banki a Najeriya da suke da zurfin karatu, kamar yadda mujallar Bloomberg ta wallafa.
Aikin banki
Umeoji ta fara aiki a bankin Zenith ne a shekarar 1998, kuma tun shigarta bankin ta jagoranci tawagar talla ta reshen Maitama kuma ta zama mataimakiyar shugabar shiyyar Abuja.
Sannan ta zama babbar darakta a Abuja da shiyyoyin bankin na 'Middle Belt'. An nada ta a kwamitin hukumar gudanarwar bankin a ranar 9 ga Oktoba, 2012.
Rayuwar zamantakewa
Bayan aikin banki, Umeoji ta kafa kungiyar ma'aikatan banki 'yan Katolika ta Najeriya (CBAN), wani dandali da take amfani da shi don inganta aikin banki da kuma hidima ga bil'adama.
Ta kasance jakadar zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya (UN-POLAC) da kuma rike kambun 'Lady of the Order of Knights of St. John International (KSJI).'
Kwanan nan Fafaroma Francis ya ba ta lambar yabo ta 'Papal Knight of the Order of St. Sylvester.'
Kyaututtukan gwamnati
A shekarar 2022, gwamnatin tarayya ta karrama ta da lambar yabo ta OON domin ya yaba irin gudunmawar da ta bayar wajen gina kasa.
Bankin Zenith ya wallafa cewa Umeoji ta lashe lambar yabo ta The Humanitarian Services Icon of the Year Award 2023 wadd The Sun ta bayar a ranar Asabar, 17 ga Fabrairu, 2023.
Dukiyar da ta mallaka
Alkaluman bayanan kudi na bankin Zenith sun nuna cewa Umeoji tana da hannun jari na kai tsaye da ya kai 68,873,169 da kuma wani hannun jarin na miliyan 1,710,123.
Darajar hannun jarin a ranar Talata, 19 ga Mayu, 2024, ya kai Naira biliyan 2.69. Ana sa ran ƙimar kudinta ta fi haka yawa idan aka yi la'akari da wasu kasuwancin da take yi.
Dan crypto ya tafka asarar $62,000
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa wani matashi mai harkar crypto ya rasa dukkanin kudin da ya mallaka a rayuwarsa bayan da farashin BTC ya fadi kasa.
An ruwaito cewa matashin ya yi amfani da $62,000 wajen sayen wani sulalla na PEPE da zummar zai samu kudi masu yawa, amma kasuwar ta juya masa baya.
Asali: Legit.ng