Dole Zenith Bank ta yi mana Bayani- Abati

Dole Zenith Bank ta yi mana Bayani- Abati

Tsohon mai Magana da yawon Tshohon Shugaban Kasa Goodluck, wato Reuben Abati ya bara dangane da hotunan da ke yawo a yana gizo na wani ma’aikacin bankin Zenith day a tsugunna gwiwa a kas a gaban Gwamnan Ekiti Ayo Fayose.

Dole Zenith Bank ta yi mana Bayani- Abati

Hotunan sun wasu da ake zargin Ma’aikatan Bankin Zenith a lokacin da suke magiya ga Gwamna Ayo fayose  sun yawaita ne a yanar Gizo a ranar Alhamis 23 da watan Yuni. Kamar yadda shi gwamnan ya fada, y ace sun zo ne Su roke shi kuma su bashi hakuri kan takaddamar da ta kunno kai wanda Bankin ya taimaka ma Gwamnan a zaben day a lashe na shekara 2014. Alhali kuma wadannan hotunan sun bazu ne bayan Bankin ta karyata maganan kashe ma Fayose kudi a a zaben shekara 2014 a Jihar Ekiti.

A ranan 20 ga watan June ne Hukumar EFCC ta rufe asusun Banki 2 na Ayo Fayose dangane da binciken da kudaden Ofishin Tsohon mai bada shawara akan tsaro wato Sambo Dasuki, inda ake zargin shi Fayose ya amsaN4.7bn a lokacin kamfe na Gwamnan a 2014. Duk da haka Fayose ya danganta mafi yawanci kudin kamfe din sa daga Bankin Zenith yazo.

Hotunan ma’aikatan Bankin Zenith a ziyara da suka kai wa Gwamna Fayose sun matukar bata ma yan Najeriya rai. Shi ko Abati ya bukaci Bankin Zenith dasu bayar ma yan Najeriya gamsassun Bayanai. Ya daura hoton a facebook din sa in day a kara da cewa “

Idan wannan gaskiya ne, toh muna bin Bankin Zenith bashin bayani, muna jita mu gani idan zasu yi nuna dattaku, akwai …..”

Wasu daga cikin masu bibiyan shafin Abati na facebook, sun nuna bambancin ra’ayi game da wannan kamari, wani mai suna Emmanuek Godwin ya ceai babu wata shedar ta bayyane mai nuna cewa wadanda suka durkusa gwiwa kasa na tare da Gwamnan ne, wasu kuma sun ce dama ai akwai yaronta a al’amuran Fayose.

Wani Adeyemi Rotimi ya ce ai ba wani sabon abu bane Bankuna su rika daukan nauyin yan siyasa, kuma Fayose ba shi ne na farko ba aka dauke nauyin sa, akan menene EFCC ke haramta hakan a Nijeriya? Ya kara da cewa idan muka lura da kyau, zamu gane cewa akwai Gwamnonin APC da yawa wadanda ita Bankin Zenith ta dauki nauyin su.

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: