2024: Ƙasashe 45 da Ƴan Najeriya Za Su Iya Zuwa Ba Tare da Biza Ba
- Najeriya ta ƙara samun daraja a jerin ƙasashen da ke ta ƙarfin fasfo, wanda ke ba ƴan ƙasar wani tagomashi yayin tafiye-tafiye zuwa turai
- Wani sabon kididdiga da shafin Henley Passport Index ya fitar, ya nuna cewa yanzu Najeriya ta koma ta 95 a ƙasashe 104 masu ƙarfin fasfo
- Legit Hausa ta tattaro bayani kan jerin kasashe 45 da ƴan Najeriya za su iya zuwa ba tare da sun yi amfani da biza ba, sai dai da fasfo kawai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Shafin Henley Passport Index, wanda ya lissafa wasu fasfo mafi karfin iko a duniya, ya ce 'yan Najeriya na da kasashe kusan 45 da za su iya zuwa ba tare da biza ba, kawai za su yi amfani ne da fasfo dinsu.
Wannan dai na kunshe ne a cikin sabon jaddawali wanda ya nuna cewa Najeriya ce ta 95 a cikin kasashe 104 masu karfin fasfo.
Fasfo din Najeriya ya kara daraja a duniya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanan Henley Passport Index galibi na dogara ne akan kebantaccen bayanai daga kungiyar sufurin jiragen sama ta duniya (IATA). u and Haiti, Leadership News ta ruwaito.
Bisa kididdigar da aka yi, Najeriya ta wuce Gana, Guinea, Kenya, Lesotho, Moroko, Benin da Namibiya wadanda ke a matsayi na 76, 83, 67, 65, 71, 79 da 65.
Kasashe 45 da ‘yan Najeriya za su iya zuwa da fasfo ba tare da biza ba:
- Barbados
- Benin
- Burkina Faso
- Burundi
- Kambodiya
- Kamaru
- Tsibirin Cape Verde
- Chadi
- Tsibirin Kamoro
- Tsibirin Cook
- Cote d'Ivoire
- Djibouti
- Jamhuriyar Dominican
- Fiji
- Gana
- Guinea
- Guinea-Bissau
- Haiti
- Iran
- Kenya
- Kiribati
- Lebanon
- Laberiya
- Madagaska
- Maldives
- Mali
- Mauritiana
- Mauritius
- Micronesia
- Montserrat
- Mozambique
- Nijar
- Niue
- Tsibirin Palau
- Rwanda
- Samoa
- Senegal
- Sierra Leone
- Somaliya
- St. Kitts da Nevis
- Gambiya
- Timor-Leste
- Togo
- Tuvalu
- Vanuatu
Jerin ƙasashe 5 da ya kamata ku ziyarta a 2024
A wani rahoton, Legit Hausa ta tattaro bayani game da wasu kasashe wadanda ya kamata ace ƴan Najeriya sun ziyarta a 2024 don yawon bude ido.
Wadannan kasashen wadanda suke cike da al'adu masu burgewa, gine-gine masu ban sha'awa, na neman masu yawon bude ido su ziyarce su don ganin abubuwan ban mamaki.
Asali: Legit.ng