An Kwashi ’Yan Kallo Yayin da Ango da Amarya Suka Kira ’Yan Sanda Aka Kama Mai Rabon Abinci
- Wani faifan bidiyo ya nuna wata dirama da aka tafka a wajen daurin aure bayan da aka kama wata mai rabon abinci tana satar abincin bikin
- An jefa baƙi da masu fatan alheri cikin tsananin mamaki bayan an gano abin da ya faru da abincin da aka ware masu
- Yayin da wasu masu amfani da yanar gizo suka nuna rashin jin dadin yadda aka kama mai rabon abincin, wasu kuma sun goyi baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
An shiga rudani a wajen wani biki yayin da aka kama wata mai rabon abinci da laifin satar abincin da ma'auratan suka siya don rabawa baki.
A cewar @favour_gist, mai rabon abincin ta hana bakin da aka ce ta kaiwa, ta boye da zummar guduwa da shi.
Akan yadda aka bankado mugun nufin mai rabon abincin, wata muryar mace a cikin faifan bidiyon @favour_gist ta bayyana cewa an yanka shanu uku a wajen bikin auren.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lokacin da aka fahimci mutane da yawa ba su samu abincin ba, sai aka fara yin bincike har aka gano inda ta boye abincin a wasu manyan kuloli.
Mutane sun yi sharhi kan wannan bidiyo da ya yadu a shafin TikTok.
Kalli bidiyon da ke a ƙasa:
Abin da mutane ke cewa:
Mummy J ta ce:
"Na san akan dan debi abincin kadan a kai gida kamar yadda aka saba, ga shi garin son banza sun ja an kama su."
Nas ta ce:
"A bikina ba zan damu da wanda ya saci abinci ba, ma damar ina cikin farin ciki a wannan ranar."
Maks ya ce:
"Ni wanda na gani, mai rabon abinci ta cika babbar kula da soyayyen kaza. Lokacin da za ta je ta saka a bayan motamutane suka kama ta."
teefah_ ta ce:
"Zan hada sojoji tare da masu raba abinci a ranar bikin aure na. Na ga ta yadda za ka boye abinci a ranar."
Tsadar abinci: An gudanar da zanga-zanga a jihar Oyo
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa maza da mata sun fita zanga-zagar lumana a jihar Oyo don nuna adawa kan tsadar rayuwa da ake fama da ita a Najeriya.
Masu zanga-zagar sun nemi shugaban kasa Bola Tinubu da ya tuna da irin alkawurran da ya dauka lokacin yakin neman zabe na cewar talaka zai ji dadi a mulkinsa.
Asali: Legit.ng