Biki Bidiri: Dan Najeriya Ya Shirya Angwancewa da ’Yan Mata 3 a Rana Daya

Biki Bidiri: Dan Najeriya Ya Shirya Angwancewa da ’Yan Mata 3 a Rana Daya

  • A yayin da wasu ke kukan wahalar dawainiya da iyali, wani matashi ya shirya angwancewa da mata uku a rana daya
  • An ruwaito cewa, yau Laraba, 31 ga watan Janairu ne matashin mai suna Tersugh Aondona zai auri matan a jihar Benue
  • Takardar gayyatar auren ta bayyana sunayen 'yan matan kamar haka; Blessing, Nancy da kuma Sulumshima

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da bakwai a aikin jarida.

Jihar Benue - Wani dan Najeriya mai suna Tersugh Aondona zai auri mata uku a rana daya a jihar Benue.

An ce za a daura auren ne a ranar Laraba, 31 ga watan Janairu (yau) a makarantar sakandare ta Lante Kukwagh, Jato-Aka, a karamar hukumar Kwande.

Kara karanta wannan

Mai gadin makaranta a Kano ya dauki ransa a cikin aji saboda tsohuwar matarsa ta sake aure

Dan Najeriya ya angwance da 'yan mata uku a rana daya.
Dan Najeriya ya angwance da 'yan mata uku a rana daya. Hoto: Harry Nyam
Asali: Facebook

Takardar gayyatar auren ta kuma bayyana sunayen matan da zai aura da suka hada da Blessing, Nancy da Sulumshima.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bikin Aondona ne mafi girma a Benue - Nyam

Za a fara shagalin bikin ne da karfe 6 na yamma har zuwa wayewar gari, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Wani Harry Nyam, wanda ya fara sanar da bikin auren a Facebook, ya rubuta cewa:

"31 ga Janairu da ake jira ta zo. Yau zamu dunguma zuwa Jato Aka don bukin abokinmu, Tersugh Aondona da aka fi sani da Aterry-baba.
"Alama ta nuna an shirya bikin aure mafi girma da aka taba yi a jihar Benue. Ina taya ka murna da kai da matanka. Ya ubangiji mu sai yaushe?"

Abin da mutane ke cewa game da auren Aondona

Wani James Atsa'am shima ya rubuta cewa:

Kara karanta wannan

Yadda ma'aikacin banki ya yi karyar 'yan bindiga sun sace shi saboda bashin naira miliyan 1.7

"Haka al'amura suke, 'yan matan nan uku da mai gidansu sun yi abin da ya faranta musu rai. Ci gaba da gashi kawai Tersugh Aondona."

Wani mai amfani da kafar, Waalawa Mbaikyor, ya wallafa cewa:

"A cikin matan uku, daya ana kiranta Wan Utyomdu-Ihyarev, daya Wan Mbaterem Ukum sai daya Wan Mbape Tor Ajio Ishangev-Ya."

Ga abin da Harry Nyam ya wallafa:

Ana hasashen tawagar Najeriya za ta lashe kofin AFCON 2023

A wani labarin kuma, wani kamfani mai suna Opta supercomputers ya yi hasashen cewa tawagar Najeriya ta Super Eagles ce za ta lashe kofin AFCON da ake buga wa yanzu.

Rahoton hasashen na bazuwa ne jim kadan bayan da aka fitar da tawagar Senegal da Moroko daga gasar cin kofin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.