"Ku Nemo Min Ita": Bidiyon Wata Daliba Tana Sallah a Kan Hanya Ya Dauki Hankulan Jama'a
- An bayyana mabanbantan ra’ayoyi biyo bayan faifan bidiyon wata ɗaliba sanye da kayan makaranta tana sallah a kan hanya
- Ta yi amfani da jakar makarantarta kamar tabarma yayin da take bin sallar da ake jiyo sautinta a cikin lasifika daga wani masallaci
- Mutane da yawa a yanar gizo sun ji daɗin yadda yarinyar ta nuna riƙo da addini tare da yaba mata kan hakan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
A cikin wani faifan bidiyo da ke ci gaba da jan hankali, an nuna wata ɗaliba musulma tana sallah sanye da kayan makaranta a kan hanya.
Ba a bayyana ko tana kan hanyar zuwa ne ko dawowa daga makaranta ba, amma riƙo da addininta ya narkar da zukatan yawancin masu amfani da yanar gizo.
A cikin faifan bidiyon, ɗalibar ta yi amfani da jakar makaranta kamar tabarma, inda take bin sallar da ta ke jiyo sautinta daga lasifikar wani masallaci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
@sarhmymoore ne ya sanya faifan bidiyon a kan TikTok kuma mutane da dama sun kalli bidiyon.
Mutane sun bayyana ra'ayoyinsu game da bidiyon
Eri imole promise page ya rubuta:
"Allah zai karɓi addu'ar ki, ni ba musulmi ba ne."
nafiudanladi480 ya rubuta:
"Allah ya karɓi addu'oin mu, ƴan uwana don Allah kar ku ga laifinta."
konibaje3 ya rubuta:
"Na rantse sai da na zubar da hawaye daga idona. Me yasa ba za ka yarda da Allah ba? Allah ya sanya mata albarka."
Wanjiru wa passion ya rubuta:
"Wayyo gaskiya na so hakan sosai, ina ma zan iya zama Musulmi, wannan imaninta ya kai, ni ba Musulmi ba ne amma Allahu Akbar."
Haykay_Global ya rubuta:
"Don Allah a taimaka min na gano wannan yarinyar, zan ba ta N50,000."
Ɗalibai Sun Ziyarci Tsohon Malaminsu
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu tsofaffin ɗalibai sun kai ziyara ga tsohon malaminsu a ranar da yake murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Ɗaliban sun yi wa tsohon malamin ma su sha tara ta arziƙi domin nuna godiyarsu kan yadda ya yi ɗawainiya da su a baya.
Asali: Legit.ng