"Gwanin Ban Sha'awa": Bayan Shekara 31 Dalibai Sun Ziyarci Tsohon Malaminsu, Sun Yi Abun Ban Mamaki

"Gwanin Ban Sha'awa": Bayan Shekara 31 Dalibai Sun Ziyarci Tsohon Malaminsu, Sun Yi Abun Ban Mamaki

  • A bikin zagayowar ranar haihuwarsa, wani malami ya sha mamaki daga ɗalibansa bayan shekara 31
  • Bayan sun isa gidansa, tsofaffin ɗaliban sun sanya ranar ta zama wacce ba zai taɓa manta wa da ita ba saboda abin da suka yi
  • Wani faifan bidiyo mai sosa rai da ke nuna manya-manyan kyaututtuka da abubuwan mamaki da suka yi masa ya narkar da zukata a intanet

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Wani faifan bidiyo mai sosa zukata ya nuna lokacin da wasu tsofaffin ɗalibai suka yiwa tsohon malaminsu abin mamaki a ranar haihuwarsa.

A cewar @surprisemadam wanda ya sanya bidiyon haɗuwar malamin da ɗaliban, ya ce sun tuna da malamin bayan shekara 31.

Dalibai sun tuna da malaminsu
Dalibai sun tuna da malaminsu bayan shekara 31 Hoto: @surprisemadam
Asali: TikTok

Suna isa cikin faifan bidiyon, suka yi masa ruwan tsaraba daban-daban a gidansa. Alamu sun nuna cewa musamman suka yi kwangila da wani kamfani domin gudanar da wannan abin mamakin.

Kara karanta wannan

Ana dab da Kirsimeti Shugaba Tinubu ya aike da sako mai ratsa zuciya ga yan Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An miƙa masa wani ɗan littafi na musamman da kek ɗin kuɗi. An kuma ba shi kyautar N700k, da dai sauran abubuwan da ɗaliban suka sanya domin tunawa da ranar haihuwarsa.

Malamin ya ji daɗin ganin tsofaffin dalibansa.

Ƴan soshiyal midiya sun yi martani

Anne ta rubuta:

"Ya Allah a matsayin mu na masu karantarwa ka sanya yaran mu da muke karantawa su tuna da mu watarana saboda abu mai kyau."

Body secrets by Aduke ta rubuta:

"Wannan yana da kyau sosai, tabbas ya kasance uba a gare su. Kamar yadda malamina Dr Adegboyega na sashen tattalin arziƙi a OOU."

user8393545994452 ya rubuta:

"Ina fatan malamina na firamare 5 rayuwa ta ladabtar da shi da wata fuskarsa can."

Ope Aderogba ya rubuta:

"Tabbas ya kasance malami mai kirki a gare su da har za su tuna da shi bayan shekara 30."

Kara karanta wannan

Kotun koli na shirin yanke hukunci, wasu tsageru sun yi yunƙurin ƙona gidan gwamnatin Kano

user9146437352374 ya rubuta:

"Ina ma ace malamata ta turanci ta ga wannan bidiyon ƙila jikinta ya yi sanyi kaɗan."

Matashi Ya Tashi Kan Yan Ƙauyensu

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani matashi ya tashi kan mutanen ƙauyensu bayan ya isa ƙauyen cikin wani yanayi na ban mamaki.

Matashinnya dira cikin ƙauyen da wata motarsa mai buɗaɗɗen sama wanda hakan ya sanya ƴan ƙauyen yin dafifi domin kallonsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng