Kwarya Ta Bi Kwarya: Sarauniyar Kyau Ta Duniya Za Ta Angwance da Attajirin Saurayinta Dan Najeriya
- Mitchel Ihezue, sarauniyar kyau ta duniya daga Najeriya ta shirya angwancewa da hamshakin dan kasuwa kuma dan siyasa, Yarima Ukachwukwu
- Mitchel dai na da shekaru 26 a duniya yayin da saurayin nata Yarima Nicholas Ukachukwu ke da shekaru 57 a duniya
- Sarauniyar ta wallafa wasu zafafan hotunan kafin aure da ta dauka da saurayin nata a shafinta na Instagram wanda ya ja hankulan jama'a
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Mitchel Ihezue, mai shekara 26 da ke rike da kambun wacce ta fi kowa kyau a duniya daga Najeriya ta shirya auren masoyinta Yarima Nicholas Ukachukwu, dan kasuwa kuma dan siyasa.
Duk da sanar da saka ranar aurenta kwanaki hudu da suka gaba, ba a bayyana kamannin mutumin ba, har sai a ranar Talata, 5 ga watan Disamba.
Shafin Withinnigeria ya ruwaito yadda aka yaye hijabin da aka saka wa angon, inda aka gano ashe Yarima Nicholas Ukachukwu ne, wanda aka fi sani da Ikukuoma,
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ikukuoma ya kasance hamshakin dan kasuwa wanda ke da 'ya'ya biyar, kuma ya rasa matarshi shekaru uku da suka gabata, tana da shekaru 41, rahoton The Nation.
Yarima Nicholas shi ne shugaban rukunin kamfanonin SNECOU kuma tsohon dan majalisar Najeriya karkashin jam'iyyar APGA.
Duba zafafan hotun a kasa:
Sarauniyar kyawawan ta wallafa a shafinta na Instagram tare da hotunan cewa:
"Wannan jinin jikina ne."
A wata wallafar kuma ta ce:
"I K U K U O M A - Saura kwana daya"
Murnar karin shekara: Rahama Sadau ta cika shakara 30 a duniya
A wani labarin, fitacciyar jarumar fina-finan Hausa (Kannywood) da na Kudu (Nollywood) Rahama Sadau, ta saki wasu zafafan hotuna yayin da ta ke murnar cika shekara 30 da haihuwa.
Rahama Sadau ta yi kaurin suna a masana'antar Kannywood bayan fitowa cikin manyan fina-finai da suka hada da Rariya, Gani ga Wane, Jinin Jikina da sauran su, rahoton Legit Hausa.
An haifi Sauda a ranar 7 ga watan Disam, 1993 a jihar Kaduna, kuma tauraruwarta ta fara haskawa bayan fitowa a fim din Gani ga Wane a shekarar 2013.
Asali: Legit.ng