Matashi Ya Shiga Damuwa Bayan Budurwarsa Ta Ki Amsa Tayin Aurenta da Ya Yi a Bainar Jama'a
- Wata budurwa ƴar Najeriya ta zama abin magana bayan ta ƙi karɓar zoben neman aurenta da saurayinta ya ba ta a ranar kammala karatunta
- Abun mamaki kuma budurwar ta karɓi hoton da yayi mata sannan ta bar shi kan gwiwoyinsa cike da takaici
- Bidiyon ya yaɗu sosai inda aka yi ta tafka mahawara a tsakanin ƴan soshiyal midiya kan wannan matakin da ta ɗauka
Saurayin da ya yanke shawarar kai soyayyarsa da budurwarsa zuwa mataki na gaba, ya fuskanci wulaƙanci a ɓainar jama'a.
A cikin wani faifan bidiyo da @viviannkym ta sanya akan manhajar TikTok, an nuna saurayin a durƙushe, yana nemar yardar budurwarsa ta amince ta aure shi a ranar kammala karatunta.
Amma, a maimakon ta karɓi zoben neman aurenta da ya yi, budurwar ta zaɓi ta karɓi ƙatoton hoton da ya yi mata kawai daga gare shi, inda ta bar ƙawayenta suna ƙoƙarin shawo kan ta.
Budurwa ta ƙi amsa tayin mai neman aurenta
Bayan abin da budurwar ta yi ba zato ba tsammani, saurayin ya tsaya a ƙasa cike da takaicin wulaƙancin da ya sha.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ƙasan bidiyon an rubuta:
"Anti ta yarda ta karɓi hoto amma Anti ta ƙi yarda ta karɓi zobe. Ku ji tsoron wannan jinsin nawa. Shiri ya lalace a ranar kammala karatu."
Ƴan soshiyal midiya sun yi martani
Masu amfani da yanar gizo sun shiga sashin sharhi don bayyana ra'ayoyinsu game da matakin da budurwar ta ɗauka.
Wasu dai sun ce abin da budurwar ta aikata bata kyauta ba, yayin da wasu ke ganin kamata ya yi ta karɓi zoben sannan ta gaya masa matsayinsa idan sun keɓe ba a bainar jama'a ba.
Ga kaɗan daga ciki:
EmmaGiddim11 ya rubuta:
"Ranar da zan je neman aure wajen budurwata, da adda zan je domin ana samu matsala jikinta ya gaya mata."
@exaddaora ya rubuta:
"Ba ka da tabbacin cewa budurwarka za ta amince maka, amma ka bayyana buƙatarƙa a bainar jama'a. Ka ba ni kunya."
@princess ta rubuta:
"Samari ina ba ku shawara, kafin ku je neman aure wajen ƴan matan ku, ku riƙa bugun ruwan cikinsu a hankali a hankali domin sanin za su amince ko ba za su amince ba, domin gujewa ɓacin rana."
@Esther love ta rubuta:
"Idan ni ce zan karɓi zoben sannan zan gaya masa gaskiyar abin da ke raina idan muka koma gida."
Budurwa Ta Raba Gari da Saurayinta
A wani labarin kuma, wata budurwa ta yanke shawarar ba za ta iya cigaba da soyayya da saurayinta ba, inda rabu da shi.
Budurwar ta bayyana cewa saurayin na ta kullum ba ya da aiki sai cin biredi wanda hakan bai kwanta mata a rai ba.
Asali: Legit.ng