Saurayi Ya Tsaya A Cikin Rana Yayin Da Budurwarsa Ta Je Tattaunawa Da Attajiri, Bidiyon Ya Yadu
- Wani matashi ya burge mutane bayan budurwarsa ta je karbo lambar wayan wani attajiri
- Saurayin wanda dan Najeriya ne ya na tsaye a cikin rana yayin da budurwar ta je wurin mai motar
- Mutane sun yabi halin matashin da cewa ya na da fahimtar rayuwa yayin da wasu ke cewa ba shi da tabbas a kanta ne
Abin mamaki yayin da aka gano wani saurayi na jiran budurwarsa ta je karban lambar wayan wani mai mota.
Saurayin na tsaye a rana cikin hakuri yayin da budurwar ta je wurin wani mai mota su na tattaunawa, Legit.ng ta tattaro.
Meye mutane ke cewa kan faifan bidiyon?
A wani faifan bidiyo, saurayin dan Najeriya ya sha yabo a wurin mutane inda su ke mamakin hakurinshi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Karauniya Yayin Da Aka Sanar Da Sabon Farashin Gas Sabanin Yadda Tinubu Ya Yi Alkawari A Baya, Bayanai Sun Fito
Yayin da wasu ke caccakar matashin ganin yadda budurwar ta ci mutuncinshi ya na tsaye ya na kallonsu da wani.
Ku kalli bidiyon a kasa:
Halin da saurayin ya nuna ya tabbatar da muhimmancin hakuri da juriya.
Wasu mutane kuma a bangarensu sun yi zargin ko matashin ba shi da kwarin gwiwa a karan kansa ne.
Martanin jama'a kan bidiyon saurayin da budurwarsa:
@hypeman_lyte:
"Saurayin ya na fahimta, mu na ganin abu da yawa."
@adedoyin.gram:
“Ko ba komai shi ba dan bakin ciki ba ne, kuma ba mai taurin kai ba."
@sharon.chigozirim:
“Kada ki bari saurayinki ya hana ki ganawa da mai aurenki."
@aver nessa:
"Tabbas ya na son ci gabanta, ba shi da bakin ciki."
@iamnaniboi:
“Allah sarki, wannan akwai karfin fahimta."
@sweetest babyyysophie:
“Rayuwa ba wahala, ku kuke daukar hakan da zafi, ya na son ci gabanta"
@anita_dera_:
“Ko da ba na son mutum ba zan masa cin mutuncinshi ba."
Bidiyon Santala-Santalan 'Yan Mata Na Leburanci
A wani labarin, wasu 'yan mata sun ba da mamaki yayin da aka gano su a wani faifan bidiyo su na aikin leburanci.
Kyawawan 'yan matan na kwaba siminti da kuma jidon bulok don kai wa wata da ke gini a gefe.
Mutane da dama sun yabi matan da cewa ba su kashe zuciyarsu kamar saura ba su na tsammani daga samarinsu.
Asali: Legit.ng