"Kin Yi Masa Tsufa": Wata Mata Ta Sha Kora Bayan Ta Je Wajen Yan Uwan Saurayinta Mai Shekara 22

"Kin Yi Masa Tsufa": Wata Mata Ta Sha Kora Bayan Ta Je Wajen Yan Uwan Saurayinta Mai Shekara 22

  • Terryannne, wata mata mai shekara 42, ta faɗa soyayya da wani matashi mai suna Promise Karanja, wanda ta girme shi da shekara 20
  • Matar ta siya masa fili kafin su je ganin iyayensa, amma sai ta tarar da abin da ba ta yi zato ba bayan sun isa
  • Ƴan uwan matashin sun bayyana cewa ba za su taɓa bari ya aureta ba saboda tsufan da ta yi masa

An yi dirama bayan matashi ɗan ƙasar Kenya, Promise Karanja, mai shekara 22 ya gabatar da masoyiyarsa, Terryanne mai shekara 42 a gaban ƴan uwansa.

Wani mai shafin YouTube mai suna Nicholas Kioko ya raka masoyan biyu domin yi musu baiko a Kahawa ta Yamma, amma sai suka tarar da abin da ba su yi zato ba.

Kara karanta wannan

Wata Zuƙeƙiyar Budurwa Ta Amarce da Farin Mutumin da Suka Haɗu a Online, Bidiyon Ya Ja Hankali

Iyayen wani matashi sun kori masoyiyarsa
Iyayen Promise sun ki amincewa da Terryanne Hoto: Nicholas Kioko
Asali: UGC
"Ba ni da abin da zance. Wannan ita ce rabin raina. Ita ce wacce na ke ƙauna." A cewar Promise.

Abin da ƴan uwan Promise suka ce a kan Terryanne

Ya tambayi mahaifyarsa mai shekara 40 a duniya ra'ayinta dangane da soyayyarsu, amma sai ƴan uwa da abokan arziƙi suka yi magana a madadinta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Da gaske? Ba za mu yarda ba. Ta girmi mahaifiyarka. Ka tabbata kuwa, ko dai kuɗinta ne su ka ruɗe ka? Wannan ba soyayya ba ce. Wayau kawai ta ke yi maka." A cewar wata mata.

Matar ta kuma yi magana kan bambancin shekarun da ke tsakaninsu, inda ta ce:

"Wannan matar idonta ya gama buɗewa ta ga jiya ta ga yau. Ba na tunanin ya dace ka yi soyayya da ita."

Ana cikin caccakar ta su ta ko ina, sai Promise ya rike hannun Terryanne wanda hakan ya ƙara ruruta wutar faɗan da ake masa.

Kara karanta wannan

Wata Mata Ta Haifi Yara 9 Cikin Shekaru 13, Ta Ce Saura Na Nan Tafe

"Ka dai na taɓata a gabanmu. Me kake son ka nuna mana? A kan ka aka fara soyayya ne? Kana son wannan tsohuwar matar ta tsaya a gaban mahaifiyarka? A cewar matar.

Ta yi masa alƙwarin samo masa budurwa mai jini a jika wacce zai aura, sannan ta yi barazanar raba gari da shi.

Abin da Terryanne ta siya wa Promise

Haka kuma Terryanne ta bayyana cewa ta ba Promise kyautar wani fili wanda aka yi wa rajista da sunansa.

"Ya ce baya son mota" A cewarta.

Kyakkyawar Budurwa Na Neman Mijin Aure

A wani labarin kuma, wata kyakkyawar budurwa ta bazama neman mijin da za aura su raya Sunnah.

Kyakkyawar budurwar ta bayyana cewa tana da sharuɗɗa waɗanda sai wanda ke sonta ya cika su, sannan za ta iya aurensa. Daga cikin sharuɗɗan dole sai ya kasance mai albashin N300k duk wata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng