Matashi Dan Najeriya Ya Koka Kan Rashin Aikin Yi Bayan Ya Koma UK

Matashi Dan Najeriya Ya Koka Kan Rashin Aikin Yi Bayan Ya Koma UK

  • Wani matashi ɗan Najeriya ya bayyana halin ƙuncin da ya samu kansa a ciki bayan ya yi hijira zuwa UK
  • A wata wallafa da ya yi a shafinsa na TikTok, ya bayyana yadda yake shan baƙar wahala wajen samun aiki a UK
  • Mutane da yawa sun yi martani a kan bidiyon, inda da dama suka ba shi shawarar ya ƙara dagewa, yayin da wasu kuma suka bayyana irin wahalar da su ke sha

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani matashi ɗan Najeriya mai amfani da sunan @pappykraen a TikTok ya janyo cece-kuce bayan wata wallafa da ya yi a shafinsa na TikTok.

Ya bayyana yadda ya ke shan baƙar wahala wajen samun aikin yi a UK, a yayin da yake rera waƙar mawaƙin nan Asake mai suma 'Lonely at the Top.'

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Wata Kungiya Ta Bukaci Ministocin Tinubu Su Yi Murabus, Ta Bayyana Dalilanta

Dan Najeriya koka kan rashin samun aiki a UK
Matashi ya bayyana wahalar da yake shan wajen samun aiki a UK Hoto: @pappykraen/ TikTok
Asali: TikTok

Samun aikin yi na da wahala a UK

A cewar sa, samun aikin yi a can, abu ne mai matuƙar wahala ba kamar yadda wasu ke tunanin akwai sauƙi ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kuma bayyana yadda ya gayawa mutanen da ya ci bashi a wajensu cewa, yana isa UK zai biya su dukkanin basussukan da ya ci.

"Ina isa UK zan fara aiki na biya ku basussukan da ke kai na ba tare da ɓata lokaci ba." Ya bayyana a cikin bidiyon.

Pappykraen ya nuna wahalar da ake sha wajen samun nasara idan mutum ya shilla ƙasar waje.

Wallafar da ya yi a TikTok ta nuna irin wahalar mutanen da suka tsallaka zuwa ƙasashen ƙetare, su ke sha wajen samun aikin yi.

Martanin ƴan soshiyal kan bidiyon matashin

@PRINCESSADESEWALEK ya rubuta:

“Omo sai da na kwashe wata biyar kafin na fara aiki ooo, omo abubuwa ba sauƙi kamar yadda ake gaya mana."

Kara karanta wannan

Kwamishinan Yan Sanda Ya Ba Da Umurnin a Kama Sufeta Da Ya Shararawa Matukin Mota Mari

@I'm Kemisola ta rubuta:

"Nagode ma Allah mahaifina bai siyar da motarsa ba a lokacin nan, da yanzu ba zan iya siya masa wata motar ba. Abubuwa ba su da sauƙi a nan."

@Paula Tabe ya rubuta:

"Waɗanda su ke a UK ne kawai za su fahimta."

@Feranmi ya rubuta:

"Halin da na ke ciki kenan a yanzu."

Budurwa Ta Koka Kan Rashin Saurayi

A wani labarin kuma, wata kyakkyawar budurwa ta koka kan rashin saurayin da za su yi soyayya tare.

Budurwar mai shekara 23 a duniya ta bayyana cewa rashin saurayin da zai so ta yana ci mata tuwo a ƙwarya, sannan ta rasa gano inda matsalar take.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng