Musulmai Sun Yi Wa Direban Jirgin Sojojin Da ‘Yan Ta’adda Su Ka Kashe Sallar Jana’iza
- A yau ne aka birne Ibrahim Adamu Abubakar wanda jami'in sojojin sama ne da aka hallaka
- Sojan saman ya rasu ne a wani harin 'yan ta'adda yayin da su ke bakin aiki a jejin jihar Neja
- ‘Yanuwa da na-kusa da shi sun ce wannan soja mahaddacin Al-kur’ani ne kuma dalibin ilmi
Kaduna - A ranar Talata, 22 ga watan Agusta 2023, jama’a su ka yi wa Ibrahim Adamu Abubakar sallah kwanaki bayan an kashe shi a jihar Neja.
Flight lieutenant Ibrahim Adamu Abubakar ya na cikin dakarun da aka rasa a wani harin ‘yan ta’adda, shi ne matukin jirgin sojoji na MI-171.
Legit.ng Hausa ta samu labarinan birne marigayin ne a babban masallacin Haruna Danja da ke kusa da Congo a garin Zariya a jihar Kaduna.
Tun a jiya ‘yanuwa da abokan arziki su ka sanar da za ayi masa sallar jana’iza a yau.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An yi wa Sojan sallar gawa
Daily Trust ta ce babban limamin masallacin, Sheikh Muhammad Sani Gumi ya jagoranci sallar wanda ta samu halartar musulami da-dama.
‘Yanuwa, abokan arziki, abokan aiki, sojoji da fararen hula sun halarci wannan jana’iza da aka yi bayan har wasu sun cire rai da ganin gawansa.
...bayan yi masa sallar ga'ib
Kafin nan, rahoton ya ce ‘yan uwan sojan sun yi masa sallah a Gaskiya a Tudun Jukun da ke Zaria bayan an tabbatar da ya mutu a wani hari.
Malaman addini sun ce musulunci ya yi bayanin yadda ake yi wa mutum wannan sallah yayin da aka gagara samun gawarsa ko kuwa tayi nisa.
Da-dama daga cikin wadanda su ka san sojan saman da su ka zanta da mu, sun yaba da halinsa, su ka ce an yi masa shaidar zama mutumin kirki.
Har malaman addini kamar Dr. Jameel Sadis, Farfesa Mansur Yelwa da Dr. Muhammad Sani Rijiyar Lemu sun ce an yi rashin mutumin kwarai.
Shehunnan sun ce Ibrahim Abubakar mahaddacin Al-kur’ani ne kuma mai neman ilmi.
Da Legit.ng Hausa ta zanta da aminin Marigayin, Najeeb Ismail bai da komai sai yabo a gare shi.
Injiniya Najeeb ya ce Najeriya tayi babban rashi.
"Marigayi Flt Lt. Ibrahim soja ne haziƙi mai kula da aikinsa. Mutum ne da aka sani da ibada, sada zumunci da mutunta jama'a.
Najeriya ta yi babban rashi. Fatanmu Allah Ya masa rahama Ya kuma albarkaci bayansa"
- Najeeb Ismail
Yaki da Kasar Nijar
Sojojin da su ka hambarar da Mohammed Bazoum sun ce sai zuwa 2026 za su sauka daga mulki, kungiyar ECOWAS ta ce ba za ta yarda da wannan ba.
Dazu aka ji Shugaban Najeriya da jagororin kungiyar ECOWAS sun kebe a fadar Aso Rock. Zaman zai yi tasiri a kan matakin da za a dauka a kasar Nijar.
Asali: Legit.ng