Bature Ya Zo Bincike Kan Hausawa, Ya Musulunta Daga Haduwa da Shehunnai
- Dr. Andrea Brigaglia mutumin Italiya ne da ya zurfi wajen bincike a game da malam Bahaushe
- Baturen ya girma a birnin Napoli ne a Turai, amma daga baya ya gamsu ya bi addinin musulunci
- Yanzu haka Andrea Brigaglia cikakken musulmi ne wanda yake bin darikar nan ta Tijjaniya
Kano - Dr. Andrea Brigaglia baturen kasar Italiya ne wanda yake da sha’awar Hausa da Hausawa, har ya shiga bincike a game da su.
Kamar yadda ya fada da yake bada tarihin rayuwarsa, Dr. Andrea Brigaglia ya yi nazari da bincike kuma ya zauna da Hausawa sosai.
A haka ne malamin jami’ar wanda asalinsa mutumin Palermo ne a kudancin Italiya ya kware a harshen Afrikan tamkar jakin Kano.
Ganin Shehu Aliyu Harazumi
Da yake bada labari a tsakanin wasu abokan addininsa, Brigaglia ya ce da ya zo Kano a 1999 ya ci karo da Shehu Aliyu Harazumi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Maher Salga At-Tijjani ya wallafa bidiyon da aka ji wannan mutumi ya na dauko silar zamansa musulmi bayan ya tashi a Turai.
A wancan lokacin, tsohon malamin jami’a a Afrika ta Kudun bai musulunta ba, sai bayan shekaru uku, ya karbi addinin musulunci.
Baturen ya yi sha’awar rayuwar babban malamin darikar tijjaniyar nan, Marigayi Shehu Aliyu Harazumi, hakan ya jawo hankalinsa.
A shekarar 2022 na bi musulunci
Sannu a hankali a shekarar 2022, Brigaglia ya rungumi addinin, ya na mai cewa bai da uzurin da zai hana shi zama musulmi yanzu.
Tun da har ya ci karo da Bayin Allah na kwarai irinsu Bashir Buhari da Harazumi, wannan mutum ya ce zai so ya bi tafarkin da su ke kai.
Tun lokacin Brigaglia ya zama musulmi, ya maida hankali wajen zikirorin manzon Allah (SWT) kamar yadda yake a koyawar sufanci.
Bincike da nazarin Andrea Brigaglia
Binciken Dr. Andrea Brigaglia sun fi yawa a bangaren cigaban addinin musulunci a Afrika ta yamma da kuma gudumuwar Sufaye.
Masanin ya yi rubuce-rubuce a kan yadda aka kafa kungiyoyin darikar Tijjaniya a kasashen Afrika irinsu Ghana, Tunisiya da Liberiya.
Legit.ng Hausa ta kuma lura malamin ya yi bincike a kan asalin kafuwar akidar Boko Haram.
'Yan ta'adda za su kai hari a jirgin kasa
An samu labari miyagun ‘yan bindiga su na shirya kai danyen hari a jirgin kasan Abuja-Kaduna, jami'an DSS sun nakarar da NRC
‘Yan ta’addan su na son kai hari na biyu a shekara kusan daya da rabi domin samun kudin fansa ta hanyar yin awon gaba da fasinjoji.
Asali: Legit.ng