An Samu Dirama Yayinda Matashin Hukumar NYSC Daga Zaria Ya Kare a Uyo Maimakon Oyo Da Aka Tura Shi
- Wani matashi da aka tura jihar Oyo domin yi wa ƙasa hidima ya ɓuge da zuwa Uyo jihar Akwa Ibom
- Matashin ya lula har zuwa Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom daga Zaria kafin ya fahimci kuskurensa
- Masu amfani da kafafen sada zumunta sun tofa albarkacin bakunansu, inda wasu ke cewa za a mayar da shi inda aka tura shi
Wani matashi wanda Hukumar kula da matasa masu yi wa kasa hidima, (NYSC), ta tura jihar Oyo, ya yi kuskuren zuwa Uyo da ke jihar Akwa Ibom.
Matashin dai ya yi kuskuren tafiya Uyo da ke Kudu maso Gabashin Najeriya, saɓanin Oyo da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.
Matashi ɗan NYSC ya ƙare a Uyo maimakon Oyo
Matashin bai fahimci cewa ya yi kuskure ba sai bayan isarsa sansanin NYSC na Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom, inda a nan ne ya fahimci cewa jihar Oyo aka tura shi.
Tsananin Kishi: Matashi Ya Gamu Da Fushin Kotu Bayan Ya Karya Hannun Budurwarsa A Kano, Ya San Makomarsa
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Matashin dai ya taho ne daga Zaria da ke jihar Kaduna, da zummar halartar sansanin horar da matasa masu yi wa ƙasa hidima.
Wani mai suna @FotoNugget ne ya wallafa labarin wannan matashi a kafar sada zumunta ta X wato Twitter a da, wanda ya ja hankulan jama'a da dama.
Martanin masu amfani da X kan matashin da ya tafi Uyo daga Zaria
Masu amfani da kafar sada zumunta ta X, sun tofa albarkacin bakunansu dangane da wannan lamari da ya faru da matashin ɗan Zaria.
Wasu daga cikinsu sun ga laifinsa na ƙin tsayawa ya natsu domin karanta takamaiman inda aka tura shi, kafin soma tafiyar.
Ga abinda wasu daga cikinsu ke cewa:
@FotoNugget ya ce:
“Kamar dai mutumin da ya tafi India maimakon Indiana domin ganin Tinda Bane a shekarar da ta gabata.”
@Timmydennyd ya ce:
“Haka ta faru da ni wata rana da zamu haɗu da wani a Ogudu kan aikin da zan yi ma sa, yayinda na tafi Ojodu. Na sha tafiya sosai a ƙasa, inda na yi amfani da N100 da ta rage mun wajen sayan biskit 4 da ruwa.”
@iambelzeez ya ce:
“Lol! Lokacin da muke sansanin NYSC na Kuros Riba, haka wani matashi ya manta takardunsa a tashar motar Nyanya da ke Abuja, dole ya koma ya je ya ɗauko su.”
@didi_special ya ce:
“Aiko zai sha bayani har ya gaji ba tare da wata hujja ba.”
NYSC ta musanta batun tura masu bautar ƙasa zuwa Nijar
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan watsi da jita-jitar da ake yaɗawa na cewa za a tura matasa masu yi wa ƙasa hidima Nijar don gwabza yaƙi da hukumar NYSC ta yi.
Hukumar ta NYSC ta ce ko kaɗan babu ƙamshin gaskiya kan bidiyon da aka yaɗa a kafafen sadarwa da ke iƙirarin tura matasan yaƙi.
Asali: Legit.ng