"Ta Yi Kuskuren Cika Masa Tanki": Rigima Ta Kaure Tsakani Wani Da Dan Najeriya Da Mai Zuba Man Fetur
- An samu hatsaniya a wani gidan siyar da man fetur bayan mai zuba man ta cika tankin motar wani mutum da man fetur
- A cikin bidiyon, mutumin da mai zuba man fetur ɗin sun kaure da hatsaniya yayin da shaidun gani da ido suka taru domin ƙoƙarin raba faɗan da su ke yi
- Masu amfani da soshiyal midiya sun yi sharhi sosai akan bidiyon inda da dama daga ciki suka nuna ɓacin ran su kan yadda man fetur yake ɗan karen tsada
Wani mai amfani da sunan @optionscity a TikTok ya sanya bidiyon wani mutum yana ta ɓaɓatu a gidan siyar da man fetur.
A cikin bidiyon, mutumin wanda ya yi matuƙar fusata, an nuna shi yana ta yi wa mai siyar da man fetur ɗin tsiya bayan ta cika masa tankin mota tatul alhalin ba abin da ya sanya ta yi masa ba kenan.
Ya yi kwaraɗi yana faɗa yayin da sauran abokanan aikin mai zuba man fetur ɗin suka riƙe ta domin kada rigimar ta su ta koma ba hammata iska.
A cikin bidiyon an rubuta cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ta yi kuskuren cika masa tanki. Rigimar da mu ke ta ƙoƙarin sasantawa kenan."
Abin da ƴan soshiyal midiya su ke cewa kan bidiyon
Bidiyon ya yaɗu sosai a manhajar TikTok, inda mutane da dama suka nuna rashin gamsuwa da ɗabi'ar da mutumin ya nuna kan abin da ya faru.
Wasu kuma sun yi nuna da rashin haƙurin da yake da shi, yayin da wasu ke ganin cewa halin matsin tattalin arziƙin da ake ciki ne a ƙasa ya sanya shi yin abinda ya yi.
@Soti ya rubuta:
"Har sai ta gaji da yin bayani."
"Ki Na Da Kyau Sosai": Tsaleliyar Budurwa Mai Hannu Daya Ta Dauki Hankula Sosai a Yanar Gizo, Bidiyonta Ya Bazu
@Charity ya rubuta:
"Ita za ta biya ai."
@VytaminQ ya rubuta:
"Omo mu masu zuba man fetur muna ganin abubuwa. Amma na iya ɓata rai ka da a raina ni."
@Blaise Ochieze ya rubuta:
"Yanzu ka cika ma mutum tanki ya zama babbar matsala...dubi inda Najeriya ta dosa a yanzu
@Daeny ya rubuta:
“Omo na ji labarin cewa fa wasu masu zuba man da gangan su ke yin hakan."
Bidiyon Mahaifiyar Wani Katon Matashi Ya Janyo Cece-Kuce
A wani labarin kuma, mutane sun cika da mamaki bayan sun yi arba da bidiyon mahaifiyar wani ƙaton matashi.
A cikin bidiyon ƙatoton matashin ya tsaya cikin mamaki yana kallon mahaifiyarsa wacce ƴar ƙarama ce mara jiki.
Asali: Legit.ng