Kurma Ya Koka a Cikin Bidiyo Kan Rashin Samun Abokiyar Rayuwa, Ya Ja Hankulan Jama'a

Kurma Ya Koka a Cikin Bidiyo Kan Rashin Samun Abokiyar Rayuwa, Ya Ja Hankulan Jama'a

  • Wani kyakkyawan matashi ɗan Najeriya ya ja hankulan jama'a a Intanet kan ƙalubalen da yake fuskanta
  • Ya ce 'yan mata ba sa son ƙulla alaƙa ta soyayya da shi saboda cutar kurumta da yake fama da ita
  • Bidiyon da ya wallafa ya ja hankulan 'yan mata da yawa, inda wasu daga ciki suka nuna suna son ƙulla alaƙa da shi

An ce samun soyayya ta gaskiya a wannan zamani abu ne mai matuƙar wahala, duk da dai wasu na fuskantar ƙalubalen rasa mai sonsu ma gaba ɗaya.

Labari ne na wani ɗan Najeriya da ya kasance kurma, wanda ya wallafa bidiyonsa a kafafen sada zumunta inda ya bayyana cewa ya gaza samun wacce za ta so shi.

Kurma ya ce 'yan mata ba sa son yin soyayya da shi
Kurma dan Najeriya ya koka kan rashin samun masoyiya. Hoto: @parksway8
Asali: TikTok

Cutar kurumta ta hana matashin samun masoyiya

Mutumin mai amfani da sunan @parksway8 a TikTok, ya ɗora bidiyonsa ɗauke da rubutu a jikinsa, da yake cewa:

Kara karanta wannan

APC: Adamu Ya Yi Murabus Ne Bayan Ya Gano Kotu Ta Rushe Zaben Tinubu? Gaskiya Ta Bayyana

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mata ba sa son yin soyayya da ni...saboda ni kurma ne”.

Kamar yadda ya bayyana, cutur kurumta ta janyo masa rashin samun abokiyar rayuwa.

Bidiyon na sa da ya wallafa ya janyo hankulan jama'a da dama, wanda cikin ɗan ƙanƙanin lokaci sama da mutane 256,000 ne suka kalle shi.

'Yan mata da dama ne suka yaba da yanayin kyawunsa sannan kuma suka nuna muradin yin soyayya da shi.

Martanin masu amfani da kafafen sada zumunta sun yi martani

Adunni ya ce:

“So yana hana ganin laifi, Allah ya kawo maka wacce ta dace.”

adebisifolakemi86 ta ce:

“Na daɗe ina neman ka tunda dama cewa aka yi in nemo saurayi kurma.”

Medinatomolayo ta ce:

“Kar ka damu, muddun zaka iya fahimtar abubuwan da nake so.”

Mz Omma ta ce:

Kara karanta wannan

Hadi Sirika Ya Bayyana Halin Da Mutanen Da Suka Yi Hadari a Jirgi Mai Saukar Ungulu a Legas Ke Ciki

“Saboda baka haɗu da ni ba ne, ka zo mu yi soyayya.”

DADDY'S GAL ta ce:

“Ka yi haƙuri kawai dai baka samu Masoyiya ta gaskiya ba.”

Tife ta ce:

“Ina son kurame, zo mu yi soyayya tare, ka haɗu sosai.”

Magidanci ya koma yi wa matarsa kallon 'yar uwa, yana shirin rabuwa da ita

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoton wani magidanci da ya ce yanzu kallon 'yar uwa yake yi wa matarsa a don haka ne ma yake shirin rabuwa da ita.

Ya ce sama da shekara biyu da suka wuce nan baya ya ji ya daina sonta, inda yanzu haka yake shirin sakinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng