"Na Gaji Da Zaman Kadaici": Kyakkyawar Baturiya Na Neman Mijin Aure, Bidiyonta Ya Yadu

"Na Gaji Da Zaman Kadaici": Kyakkyawar Baturiya Na Neman Mijin Aure, Bidiyonta Ya Yadu

  • Wata kyakkyawar baturiya a TikTok ta bazama neman saurayin da zai so ta da zuciya ɗaya domin su yi rayuwa tare
  • Baturiyar mai suna Laura, ta bayyana cewa ta gaji da zaman ƙaɗaici haka nan domin tana buƙatar namijin da zai so ta a duk inda yake a duniya
  • Laura, mai shekara 38 a duniya ta bayyana cewa ba ta damu ba da launin fatarsa sannan shekarunsa ba matsala ba ne a wajenta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata kyakkyawar baturiya tana neman saurayin da zai so ta sannan ya nuna mata ƙauna.

Baturiyar mai suna, Laura, ta bayyana a TikTok cewa shekarunta 38 a duniya, sannan ta gaji da zama ita kaɗai babu abokin rayuwa.

Baturiya na neman mijin aure
Laura mai shekara 38 tace zaman kadaici na damunta Hoto: TikTok/@laura.s442
Asali: TikTok

Laura ta gayawa masu bibiyarta a TikTok cewa ba ta damu da daga inda wanda zai so ta ya fito ba, kawai abinda take buƙata shi ne saurayin da zai zama abokin rayuwarta.

Kara karanta wannan

Rundunar Soji Ta Bayyana Ainihin Dalilin Kama Sojan Da Ya Bar Musulunci Ya Koma Kiristanci

Ta kuma bayyana cewa shekaru ko launin fata basu daga cikin abubuwan da take dubawa, a neman da take yi na samun wanda zai zama abokin rayuwa a gareta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Baturiya mai shekara 38 na neman saurayi a TikTok

Haka kuma, kuɗi ko abun duniya basu tsolewa Laura ido ba, domin ita kawai tana son samun so ne na haƙiƙa.

Bidiyon da ta sanya a TikTok ɗin ya yaɗu sosai inda mutane da dama suka nuna cewa a shirye su ke su amsa wannan tayin na ta.

Wasu daga cikinsu har tambayar a inda take su ke yi domin bayyana kansu a gareta.

Martanin masu amfani da TikTok ya yin da baturiya ta fito neman saurayi

@Ben Jackson ya rubuta:

"Barka, ina fatan za ki lura da ni."

@GSM ya rubuta:

"Mu fara yanzu kawai."

Kara karanta wannan

Rashin Biyan Kudin Shagulgula Ya Sanya Amarya Ta Soke Aurenta Ana Saura Sati 1 Biki, Iyaye Sun Ba Ta Muhimmiyar Shawara

@user8891459442712 ya rubuta:

"Zuciya mai kyau ita ce mabuɗin nasara. Tabbas za ki haɗu da wanda ya dace."

@arkeycade ya rubuta:

"Ni kawai yakamata ki nema."

@stephenhawkyard ya rubuta:

"Ƙila wata rana ni ma na haɗu da mace mai irin wannan ɗabi'un."

Amarya Ta Soke Aurenta Ana Saura Sati 1 Biki

A wani labarin kuma wata budurwa mai shirin zama amarya ta ɗauki wani hukunci mai tsauri na soke aurenta ana saur sati ɗaya biki.

Budurwar dai ta fasa auren angon na ta ne saboda ya gaya mata cewa ba shi da kuɗin da zai ɗauki nauyin shagulgula biyar da ta shirya za ayi a bikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng