‘Yar Najeriya Ta Dawo Ta Dauki Saurayinta Zuwa Amurka Saboda Karancin Samari a Can

‘Yar Najeriya Ta Dawo Ta Dauki Saurayinta Zuwa Amurka Saboda Karancin Samari a Can

  • Wata ‘yar Najeriya da ke zaune a kasar Amurka ta dawo gida don tafiya da saurayinta zuwa can
  • An ce budurwar ta dawo ne domin tafiya da saurayinta da ta bari a Najeriya saboda ta gaza samun nagartaccen saurayi a can
  • Bayanai sun nuna cewa dama saurayin ya shafe sama da shekaru uku ba tare da aikin yi ba a daidai lokacin da masoyiyar tasa ta zo masa da wannan albishir

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata ‘yar Najeriya da ke zaune a kasar Amurka, ta dawo Najeriya domin tafiya da saurayinta zuwa can.

Budurwar ta bar saurayin nata a Najeriya a lokacin da ta koma Amurka, amma bayan da ta samu duniya, sai ta yanke shawarar dawowa domin tafiya da shi.

Wata mai suna @deenayaah, wacce kawa ce a wurin wannan budurwa, ta wallafa wannan labarin a shafinta na Tuwita.

Kara karanta wannan

“Kaina Ya Kulle”: Budurwa Ta Shiga Rudani Yayin da Saurayinta Ya Tura Mata N500k Bayan Ta Kama Shi Yana Cin Amanarta

Budurwa ta dauke saurayinta daga Najeriya zuwa kasar Amurka
'Yar Najeriya ta dawo ta dauke saurayinta zuwa kasar Amurka saboda rashin samun nagartaccen namiji. Hoto: Getty Images/Wsfurlan
Asali: Getty Images

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An ce saurayin ya kasance yana ta fama da rayuwa ba tare da aikin yi ban a tsawon shekaru uku gabanin dawowar budurwar tasa daga Amurka.

Ta koka kan cewa babu nagartattun mazaje a Amurka

Deenayah ta ce dalilin da ya sa kawarta ta dawo ta tafi da saurayin nata shi ne saboda babu mazaje masu nagarta a inda take da zama, inda ta yi nuni da cewa yana da kyau a rika daraja mazajen Najeriya.

Ta ce mazajen Najeriya na daga cikin mafiya nagarta a duk duniya, a saboda haka ya zama dole a rika daraja su.

Martanin masu amfani da Tuwita dangane da budurwar da ta mayar da saurayinta Amurka

Wasu daga cikin masu amfani da Tuwita sun tofa albarkacin bakunansu dangane da wannan budurwa da ta tafi da saurayinta zuwa kasar Amurka kamar haka:

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Fasa Auren Attajirin Saurayinta Ana Dab Da Biki, Ta Bayyana Dalilanta a Cikin Bidiyo

@SonOfaBlacksmth ya ce:

“Gobe kuma idan da zai yi tari za ku kira shi da mafi munin suna a duniya. Kafafen sada zumunta ke fada muku labaran banza dangane da kulla alakar aure. Ina fatan al'amura su daidaita a tsakaninsu."

@chi_agozie7 ya ce:

“Ta nema ba ta samu ba shi ne ta dawo wajensa”

@HabeebahMore ta ce:

"Zan dawo Najeriya in dauki saurayi na idan ya kasance yana kyautata mini."

Budurwa ta yi alkawarin bai wa duk wanda ya aureta gida, mota da miliyan 50

Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto kan wata budurwa da ta fito kafar sada zumunta ta bayyana cewa za ta yi gagarumar kyauta ga duk wanda ya aureta.

Budurwar ta bayyana cewa za ta ba wanda ya aureta kyautar gida, mota da kuma naira miliyan 50, amma da sharadin ba za a yi ma ta kishiya ba.

Kara karanta wannan

Wa Zai Auro Wani? Rikita-rikita Bayan Amarya Ta Ce Dole Sai Dai Miji Ya Koma Amfani Da Sunanta

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng