"Ku Taimaka Min Na Samu Mijin Aure": Baturiya Na Neman Mijin Aure Ido Rufe

"Ku Taimaka Min Na Samu Mijin Aure": Baturiya Na Neman Mijin Aure Ido Rufe

  • Wata baturiya mai neman mijin aure ido rufe tace za ta bayar da kyauta mai tsoka ga duk wanda ya taimaka mata ta samu wanda zai aureta
  • Budurwar mai suna Eve Tilley-Coulso, tace za ta bayar da kyautar N3.8m ga duk wanda ya samo mata wanda zai aureta
  • Bidiyon nata ya janyo cece-kuce inda ƴan soshiyal midiya suka riƙa cewa lallai budurwar ta ƙagu ta shiga daga ciki

Wata baturiya mai shekara 35 a duniya ta bayyana cewa tana neman namijin da zai aureta, kuma a shirye ta ke a haɗa ta duk wanda ya shirya.

Baturiyar mai suna Eve Tilley-Coulso, ta bayyana cewa duk wanda ya taimaka mata ta samu wanda zai aureta za ta ba shi tukwicin N3.8m.

Baturiya na neman mijin aure
Za ta bayar da kyautar N3.8m ga wanda ya samo mata miji Hoto: Eve Tilley-Coulso/NYT
Asali: UGC

Ta bayyana cewa ta sanar da ƙawayenta kan hakan, amma har yanzu sun kasa samo mata wanda zai aureta.

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Auri Attajirin Da Yake Ba Ta N50k Duk Wata, Ta Yi Korafin Cewa Ya Cika Mako

Baturiya za ta bayar da tukwicin N3.8m ga wanda ya samo mata mijin aure

Eve ta bayyana cewa yanzu ta kwashe shekara biyar kenan ba tare da saurayi ba, sannan tana buƙatar namijin da za a ɗaura musu igiyar aure.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin bidiyon wanda ya yaɗu, Eve ta bayyana cewa ba matsala ba ne ko auren ya daɗe ko bai daɗe ba, amma duk wanda ya haɗa ta da wanda za ta aura za ta ba shi N3.8m.

A kalamanta:

"Duk wanda ya haɗa ni da mijin da zan aura zan ba shi N3.8m. Ba dole sai na daɗe tare da shi ba. Za mu iya rabuwa bayan shekara 20, hakan ba matsala ba ne, amma duk wanda ya haɗa ni da wanda aka ɗaura mana aure, zan ba shi N3.8m.

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Fasa Auren Attajirin Saurayinta Ana Dab Da Biki, Ta Bayyana Dalilanta a Cikin Bidiyo

Dole ya mutumin ya kasance dogo, a cewar Eve

A dangane da irin kalar namijin da ta ke son samu, Eve ta ce ba wasu abubuwa sosai ta ke buƙata ba, amma dole ya kasance dogo ne.

Bidiyon dai an ɗora shi ne a shafin @ebtilley na manhajar TikTok.

Budurwa Ta Koka Kan Karancin Samari

A wani labarin na daban kuma, wata budurwa ƴar Najeriya mai rayuwa a ƙasar Jamus ta koka kan ƙarancin samarin da su ke fama da shi.

Budurwar ta bayyana cewa lamatin ya kai ga har kuɗi su ke biyan samari domin su riƙa kawo musu ziyara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng