"Muna Ji A Jikinmu": Budurwa Ta Koka Kan Karancin Samari, Bidiyon Ya Yadu
- Yayin da 'yan mata ke cin duniyarsu da tsinke a Najeriya, wasu na can suna kokawa a kan karancin samari
- Wata budurwa ta wallafa faifan bidiyo inda ta ce halin da suke ciki na rashin samari ya yi a kasar Germany
- Budurwar ta ce komai sai ka biya kafin ka samu saurayin da zai kawo maka ziyara hatta kudin sufuri
Wata budurwa da ke rayuwa a kasar Germany ta koka a wani faifan bidiyo kan karancin samari.
Matashiyar mai suna Queen First a faifan bidiyon ta ce sam maza ba su damu da soyayya ba a can, cewar Legit.ng.
Ta ce mata na shan wahala kan karancin samari a Germany
Ta ce 'yan mata a Germany bayan sun biya sauran abubuwa a kasar, haka suke biyan maza don su kawo musu ziyara.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ta kara da cewa har da kudin sufuri sai kin ba wa saurayi don kawo miki ziyarar soyayya, bayan haka dole ki girka masa abinci don jin dadin hira.
A cewarta:
"A matsayin mu na 'yan mata muna fuskantar matsala, gaba daya Nahiyar Turai muna fuskantar matsala, kusan komai biya mu ke, babu soyayya a nan, idan kina son saurayi kika masa magana, dole zaki biya."
Ta ce bayan kin biya ya zo, haka za ki sake biya ya koma gidansu.
Mutane da dama sun yi martani inda suka ce tabbas haka lamarin ya ke a Germany.
Ku kalli bidiyon a kasa:
Mutane sun tofa albarkacin bakinsu a kan faifan bidiyon yayin ta ke koka wa kan karancin samari.
@KingJojo:
"Ya yi kyau sosai..haka ku ke mana a Naija, ta juya ko?."
Matar Da Ta Yi Wa Maza 2 Alkawarin Aure Ta Koka a Ranar Bikinta, Saurayin Ya Hana Ta Zuwa Wajen Daurin Aure a Bidiyo
@Honey Segun:
"Lokacin biya ya yi na 'yan mata...su dandana su ma."
@MyRideordie:
"Haka muke fuskanta."
Budurwa Ta Nuna Kyautar Da Saurayinta Ya Mata Tsawon Shekaru 11 Suna Soyayya
A wani labarin, wata budurwa ta bayyana irin kyautar da saurayinta ya mata a tsawon shekaru 11 da suka yi suna soyayya.
Budurwar ta ce ba ta taba ganin mai mako a duniya ba irin saurayin nata, ta ce abubuwa uku kadai ya taba ba ta.
Ta nuna abubuwa ukun da ya taba ba ta kyauta kamar safar kafa da buroshin goge hakora sai kuma mayin wanke gahi na mata.
Asali: Legit.ng