Matar Auren Da Ta Auri Wani Attajiri Ta Koka Kan N50k Da Yake Ba Ta Duk Wata, Tace Ya Cika Mako

Matar Auren Da Ta Auri Wani Attajiri Ta Koka Kan N50k Da Yake Ba Ta Duk Wata, Tace Ya Cika Mako

  • Wata matar aure ƴar Najeriya da ta auri wani attajiti saboda kuɗinsa ta koka kan halin maƙon da mijinta yake da shi
  • Mijin nata yana bata N50k kowane wata domin ta kula da kanta inda ya gaya mata ta siya duk abinda ta ke so da kuɗin
  • Mutane da dama sun bayyana ra'ayoyinsu inda suka ɗora mata laifi kan zaɓin da ta yi na auren mai abun hannu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata matar aure ƴar Najeriya wacce ta auri wani attajiri saboda kuɗinsa ta garzaya soshiyal midiya inda ta koka kan rashin jindaɗin da ta ke yi a gidan mijinta.

Labarin matar dai an sanya shi ne a shafin Instagram na @coupletherapies inda ta ke fatan samun shawarwari daga wajen mutane.

Matar aure ta koka kan halin mijinta mai mako
Matar auren tana neman shawarar yadda za ta fuskanci lamarin Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Matar aure ta koka cewa mijnta ya cika maƙo

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Fasa Auren Attajirin Saurayinta Ana Dab Da Biki, Ta Bayyana Dalilanta a Cikin Bidiyo

Ta rubuto cewa mijinta shi kaɗai kawai yake more dukiyarsa inda ya ƙi yarda ya kashe mata kuɗi sosai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yana siyo kayan alatu masu tsada domin kansa amma ita kuwa N50k kawai yake bata a wata a matsayin kuɗin da za ta kula da kanta da su.

Matar ta bayyana cewa ba ta da wasu hanyoyin da za ta samu kuɗi saboda mijinta da kan shi yake ɓoye abincin gidan.

Ta nemi shawara kan yadda za ta sauya shi ya dawo yana nuna mata gata domin yanzu ba jindaɗin halayyar da yake nuna mata ta ke yi ba.

Labarin na ta ya sanya ƴan soshiyal midiya sun yi martani sosai a manhajar Instagram.

Wasu daga cikinsu sun caccake ta saboda ta aure shi shi domin kuɗinsa inda suka ba ta shawarar ta rabu da shi idan ba ta jindaɗin zama da shi.

Kara karanta wannan

Mmesoma Ejikeme Ta Sharbi Kuka a Yayin Wayar Tarho, Ta Dauki Alkawarin Bayar Da Hakuri, Sabon Bidiyo Ya Bayyana

Wasu daga ciki kuwa sun ba ta shawarar ta fara kasuwanci ko ta nemin aikin yi domin ta dai na dogara da shi cewa sai ya yi mata komai.

Budurwa Ta Fasa Auren Attajirin Saurayinta

A wani labarin na daban kuma, wata budurwa ta fasa auren attajirin saurayinta an dab da bikin aurensu.

Budurwar ta bayyana cewa halayyar da yake nuna mata wacce ba ta jindaɗin hakan ya sanya ta yanke shawarar rabuwa da shi duk da yana da kuɗi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng