Bayan Matarsa Ta Tsere: Wani Ya Auro Mata 3 A Rana Daya Don Huce Takaici, An Yi Gagarumin Biki

Bayan Matarsa Ta Tsere: Wani Ya Auro Mata 3 A Rana Daya Don Huce Takaici, An Yi Gagarumin Biki

  • Wani mutumin Shanwe da ke yankin Katavi a Tanzania ya girgiza mutane saboda abin da ya aikata
  • Athuman Yengayenga ya auri mata uku a rana daya saboda huce takaicin guduwa da matarsa ta yi ta bar shi
  • Ya ce ya so ya auri mata hudu saboda ko da wata ta gudu zai tsira da sauran ba tare da shiga matsala ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani mutum ya kashe jama'a da mamaki inda ya auri mata uku a rana daya a wani gagarumin biki.

Athuman Yengayenga ya shiga masallaci da zankada-zankadan 'yan mata da nufin aurensu gaba daya, Legit.ng ta tattaro.

Bayan Matarsa Ta Tsere: Wani Ya Auro Mata Uku A Rana Daya Don Huce Takaici, An Yi Gagarumin Biki
Mutumin Tare Da Mata Ukun Da Ya Auro A Rana Daya A Wurin Biki. Hoto: AZAM TV.
Asali: UGC

Yengayenga wanda mazaunin Shanwe ne da ke yankin Katavi a Tanzania, ya ce ya yi niyyar auren mata hudu saboda bacin rai.

Ya ce ya auro mata uku a rana daya ne don huce takaici

Kara karanta wannan

“Buhun Siminti N5k Ne Yanzu”: Matashi Ya Kalubalanci Mai Aikin Gini Da Ya Sha Alwashin Kera Hadadden Gida Da N5m

Ya ce matarsa da suke tare ta gudu ta barshi shiyasa ya auri mata hudu don huce haushi, cewar AZAM TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin hikimarsa shi ne idan ya auri mata da yawa, ko da daya ta gudu zai tsira da sauran.

Matan nasa Fatuma Rafaeli da Asha Pius da Mariam John sun bayyana yadda suke ji da auren namiji daya.

Sun tabbatar cewa dole a samu kishi tun da dukkansu 'yan Adam ne, amma za su yi kokari don samun zaman lafiya a tsakaninsu.

Matan sun bayyana yadda suke ji da auren

Cewar uwargida Fatuma, yayin da ta ke gyara hijabinta:

"Har yanzu ba mu cika ba, muna bukatar mace guda daya."

Mafi yawan 'yan uwan Yengayenga suna auren mata da yawa, hakan ba wani abin mamaki ba ne a al'adarsu.

Amma auren mata uku a rana daya ya yi matukar ba wa 'yan uwan nasa mamaki saboda ba su saba gani ba.

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Yi Wa Samarinta 3 Dabara, Sun Zo Gaba Daya Sun Tayata Kwashe Kaya Zuwa Sabon Gida

Rikita-Rikita Yayin Da Amarya Ta Ce Sai Dai Ango Ya Makala Sunanta A Nasa

A wani labarin, wasu da ke shirin yin aure sun girgiza mutane yayin amaryar ta bukaci babban abu a gun ango.

Amaryar ta ce dole mijin ya makala sunanta a nasa kamar yadda suma matan ke yi idan sun auri maza.

Ta samu shawara daga wata mai bahasi akan harkar aure, inda ta ce mata bai kamata ta bukaci hakan ta wannan sigar ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.