Rikita-Rikita Yayin Da Amarya Ta Ce Sai Dai Ango Ya Makala Sunanta A Nasa, An Ba Su Shawara
- Wasu ma'aurata da ke shirin angwancewa sun shiga rikita-rikita ana daf da daurin aurensu
- Amaryar ta bukaci angon ya dauki sunanta na biyu ya makala a nasa sunan, angon ya ki yarda
- Mafi yawan mata kan sauya sunansu na biyu zuwa na mazajensu, yayin da wasu ke amfani da nasu na asali
Mafi yawan ma'aurata na rikicewa kan wani suna ya kamata su dauka bayan sun yi aure, inda mafi yawan mata ke daukar na mazajensu.
Yayin da wasu ke ci gaba da amfani da sunansu na asali wasu kuma na kokarin daukar na mazan da za su aura.
Har ila yau, akwai masu kirkirar sabon suna don ci gaba da amfani da shi, kamar yadda Legit.ng ta gano.
Yadda Amarya ta tada kayar baya akan saka sunanta a na angonta
Wasu da ke shirin yin aure sun shiga rikita-rikita yayin da amaryar ta ce dole mijin ya sauya sunansa zuwa nata.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Amaryar ta rubuta neman shawara ne a wurin Annalisa Barbieri da ke rubutu a The Guardian, don samun mafita yayin da ta ce angon ya ki yadda da shawarar nata kwata-kwata.
Barbieri ta ba ta shawarar cewa bai kamata ta bukaci haka ba, sai dai ta zauna da shi don samun maslaha da kuma bayyana masa bukatunta.
An ba ta shawarar yadda za ta bi da al'amarin cikin lumana
Ta shawarce su da su yi amfani da sunansu, ko su kirkiri sabbin sunaye ko kuma su yi amfani da duka biyun.
Amma ta ce yin amfani da suna daban da na 'ya'yansu zai iya haifar da matsala yayin tafiye-tafiye.
Matar Da Ta Yi Wa Maza 2 Alkawarin Aure Ta Koka a Ranar Bikinta, Saurayin Ya Hana Ta Zuwa Wajen Daurin Aure a Bidiyo
Ta shawarci amaryar da ta yi koyi da yadda aure yake a wurinta, yayin da ta ce aure wata dama ce ta inganta al'adu da kuma 'yanci.
Matashi Ya Rikice, Hannunsa Na Rawa Yayin Duba Sakamakon Jarrabawar 'JAMB'
A wani labarin, wani matashi ya ba da mamaki yayin da yake duba sakamakon jarabawarsa ta 'JAMB'.
Matashin yayin duba sakamakon hannunsa sai rawa ya ke yayin da zuciyarsa ke karkarwa.
Abokansa da ke wurin sun bukaci ganin sakamakon yayin da ta bayyana ya samu maki har 158, inda mutane suka ba shi shawarar ya shiga Kwalegin Fasaha.
Asali: Legit.ng