Matar Aure Ta Koka Bayan Babbar Kawarta Za Ta Aure Mata Miji

Matar Aure Ta Koka Bayan Babbar Kawarta Za Ta Aure Mata Miji

  • Wata matashiya matar aure ta shiga damuwa bayan mijinta ya rabu da ita bayan ta haifa masa ƴaƴa uku lokacin suna tare
  • A cikin wata wallafa da ta yi a manhajar TikTok wacce ta yaɗu, matashiyar ta koka cewa mijinta zai auri babbar ƙawarta
  • Ta bayyana cewa mijin nata bai taɓa ziyartar iyayenta ba amma har baiko yaje an yi masa da babbar ƙawarta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata matashiya matar aure ta shiga cikin matuƙar damuwa bayan mijinta ya watsata a kwandon shara bayan ta haifar masa ƴaƴa uku.

Inda abin ya ƙara taɓarɓarewa da matuƙar ciwo, a cewar matashiyar shi ne mijin nata babbar ƙawarta zai aura.

Matar aure ta shiga damuwa bayan mijinta zai auri babbar kawarta
Matar ta nuna damuwarta kan auren babbar kawarta da zai yi Hoto: TikTok/@katharine795
Asali: TikTok

A cikin wata wallafa da ta yi a manhajar TikTok, matashiyar mai amfani da sunan @katharine795 ta bayyana cewa ko sau ɗaya mijinta bai taɓa ziyartar iyayenta ba.

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Rabu Da Mijinta Bayan Ta Samu N1.5bn, Kotu Ta Umarci Ta Ba Mijin Duka Kudin, Ta Bayar Da Kwakkwaran Dalili 1

Ta bayyana cewa mijin nata ya yi dukkanin wasu abubuwan al'ada da ake yi akan babbar ƙawarta sannan har an shirya ɗaura musu aure.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Katharine ta kuma bayyana cewa mijin nata da kuɗaɗen da ta samo a ƙasar Saudiyya ne yake ta facakar shi da su.

A kalamanta:

"Babbar ƙawata za ta auri mijina wannan Asabar ɗin mai zuwa. Yanzu aurensu za a yi, amma ni ce uwar ƴaƴansa guda uku. Amma bai taɓa ziyartar iyayena ba. Yana jindaɗinsa da kuɗin da na samo a shekara uku da na yi a Saudiyya. Wata rana sai ka girbi abinda aka yi min."

Mutane sun yi tsokaci bayan magidanci ya rabu da matarsa domin auren babbar ƙawarta

@Nomier Kelly ta rubuta:

"Ba lokacin kuka, ki bi bayansa ki koya masa darasi. Wannan 2023 ce ba mu da lokacin yin kuka, ki je ki koyawa su dukansu darasi mai kyau."

Kara karanta wannan

"Ana Min Barazanar Kisa": Asari Dokubo Ya Fallasa Masu Son Ganin Bayansa a Doron Duniya

@loyongwg4ak ya rubuta:

"Ki fi ƙarfin shaiɗan ta hanyar aikata kyakkyawa, ki yi wa waɗanda suka zalunce ki addu'a, sannan kuma ki bar ramuwa a hannun ubangiji."

@dyeb0tq496fo ta rubuta:

"Eh lallai tabbas sai ya biya!!! Yakamata ki ƙarfafawa kan ki gwiwa yaranki suna da buƙatarki."

Matashiya Ta Yi Kukan Rashin Samun Miji

A wani labarin kuma, wata mata mai shekara 39 a duniys ta koka kan yadda jar yanzu ta kasa samun saurayi ballantana miji.

Matashiyar ta koka cewa rashin miji da ƴaƴa da motar hawa ta kanta ya daɗe yana ci mata tuwo a ƙwarya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng