Mercy Aigbe Ta Fadi Darasin Da Ta Koya Yayin Hajji A Makka, Mutane Sun Yi Martani Kan Bidiyon Da Ta Wallafa
- Fitacciyar ‘yar shirin fim a Najeriya Mercy Aigbe Adeoti ta bayyana irin darusan da ta kowa lokacin da take aikin hajji
- Ta bayyana cewa abin da yafi burgeta shine yadda babu bambanci tsakanin talaka da mai kudi, baki ko fari duk daya ne
- Jama’a da dama sun tofa albarkacin bakinsu inda har wadanda ba Musulmai ba suka nuna sha’awar zuwa Makkah
‘Yar fim a Najeriya, Mercy Aigbe Adeoti ta bayyana irin darusan da ta koya yayin aikin hajji a Saudiyya.
Mercy ta ce a Makkah babu banbancin arziki ko kalar fata da jinsi ko kuma shekaru, kowa duk daya ne a can.
Ta bayyana irin wahalar da ta sha yayin tafiya har ta sa’o’i biyu daga Minna zuwa Jammarat da kuma yadda suka huta kafin ci gaba da tafiya, cewar Legit.ng.
Mercy ta bayyana darasin da ta koya yayin aikin hajjin a Makkah
Ta wallafa faifan bidiyo da mijinta inda ta rubuta kamar haka:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Lokaci: karfe 1:30 na dare, Wuri: Jammarat, bayan tafiya mai wahala har ta tsawon sa’o’i biyu daga Minna zuwa Jammarat, dole muka tsaya muka cika tumbin mu da abincin kyauta kafin jifan shedan.
“Kalli yadda Alhaji @kazimaadeoti yake yalki. Makkah akwai daidaito, abin da na sake koya a garin shi ne ko yaya kake ta fannin launin fata da shekaru ko jinsi ko kai tsoho ne ko yaro, duka daya ne a wurin Allah.”
“Allah ya karbi ibadun mu da muka gabatar.”
Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu akan abubuwan da ta ce ta koya:
abu_5tb:
"Kai da kake karanta wannan zaka je hajji wata shekara.”
qumbestic14fabrics:
“Wannan Musulunci kenan, kowa daidai ne ko yaya kake, ina alfahari da kasancewa ta Musulma.”
mam_tiwa_:
“Masha Allah..kyauwan Musulunci kenan…dukkan mu daya ne a wurin Allah. Ina sonki Mami. Allah ya karbi ibada.”
kids_apparelng:
“Na ganku duka kuna dawafi bayan sallar Juma’a jiya, hajj karbabbiya.”
rabiatadekunle:
“Ameen. Tabbas wannan tunatarwa ce, cewa mu ba na musamman bane kamar yadda muke tunani…Allah ya bamu ikon yin addinin Musulunci.”
ymc_collectionss:
“Duk da yake ni ba Musulmi bane, amma ina son zuwa Makkah.”
itsjustolaa:
“Allah ya bamu ikon yin Musulunci cikin sauki.”
Hajjin 2023: Daya Daga Cikin Maniyyatan Abuja Ta Riga Mu Gidan Gaskiya A Saudiyya
A wani labarin, Hukumar Alhazai a Abuja ta sanar da rasuwar daya daga cikin mahajjatanta a Makkah.
Hukumar ta ce marigayiya Hajiya Amina Yunusa ta rasu ne yayin aikin hajji a birnin Makkah da ke Saudiyya.
Asali: Legit.ng