Karya Ba Kyau: Santaleliyar Budurwa Ta Rufe Fuskarta Don Kunya Bayan Ta Yi Wa Kawayenta Karya A Otal
- Wata santaleliyar budurwa ta sha kunya bayan kawayenta sun gano ta tana gadin wani otal
- Ta musu karyar ita ma'akaciyar otal din ne da ke tarbar baki, kwatsam sai suka kamata tana gadi
- Budurwar ta tsere da gudu tare da rufe fuskarta lokacin da ta fahimci ana nadar bidiyon ta
Wata budurwa da ke gadin otal ta sha kunya yayin da kawayenta suka iske ta a bakin aiki.
Lokacin da ta fahimci ana daukar bidiyonta sai ta arce yayin da take kokarin rufe fuskarta saboda kada a gane ta.
Budurwar ta yi karya cewa ita ce mai tarbar baki a otal din
A saman faifan bidiyon da aka gano a TikTok, an bayyana cewa budurwar ta yi wa kawayenta karya cewa ita ma'akaciyar otal din ne mai kula da baki.
“N250,000 Na Siye Su”: Mai Sana’ar Gwanjo Ta Fashe Da Kuka Bayan Ta Bude Sinkin Gwanjon Da Ta Siya, Tarkace Ne a Ciki
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mutane fiye da 800,000 ne suka kalli bidiyon, yayin da jama'a suka ba ta shawara kada ta ji kunyar aikin da take yi, Legit.ng.
Ku kalli bidiyon budurwar a kasa:
Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu tare da kara mata karfin gwiwa akan aikinta.
Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu tare da kara mata karfin gwiwa akan aikinta.
"Meyasa kike gudu? Kin yi kyau sosai, kin dace da aikin, hakan yafi kina zaman banza."
"Kada ki ji kunyar aikin da kike yi saboda idan baki da kudi babu mai taimakonki."
"Ba ku da damar daukar mutum a bidiyo ba tare da amincewarshi ba, wannan rashin mutuntawa ne da kuma kauyanci."
“Kina Karawa Addinin Musulunci Kyau”: Jaruma Mercy Aigbe Ta Nunawa Duniya Mijinta Yayin da Suke Aikin Hajji
"Ki yi alfahari da aikinki, babu wanda yasan ya gobe za ta kasance, a da ni lebura ne amma yanzu dubi abin da Ubangiji ya mini, gobe ta Allah ce, kiyi alfahari da aikinki."
"Mu da muke aikin shara a kasashen ketare, so muke mu dawo masu gadi"
"Ki so aikinki yarinya, karki gudu ko ki buya"
"Ashe abin da gaske ne, wani ya tambaye ni a kempinski akan cewa ya ji mutane suna magana akai."
"Ki yi alfahari da aikinki, yafi ki je kina roko."
Budurwa Ta Koka Bayan Saurayinta Ya Dandana Abincinta Ya Tsere, Ba Ta San Dalili Ba
A wani lanarin, wata budurwa ta bayyana yadda saurayinta ya tsere bayan ya dandana abincinta.
Budurwar ta ce saurayin nata yanzu ya yi bulokin din duk ta ko ina da yasan za ta same shi.
Asali: Legit.ng