"Kwana Hudu Da Sa'o'i 5": Matashi Dan Najeriya Da Matarsa Baturiya Sun Kafa Tarihi, Sun Yi Waya Ta Sa'o'i 101
- Wani matashi ɗan Najeriya da matarsa baturiya sun yi wani abun ban mamaki bayan sun yi hira a wayar tarho har ta sa'o'i 101
- Da su ke sanar da wannan nasarar da suka samu tare da nuna hujjoji, ma'auratan sun yi kurin cewa sun karya tarihin kundin Guinness na ma'auratan da suka daɗe suna waya
- Wannan gagarumin aikin da ma'auratan suka yi yaba mutane mamaki inda suka yi tunanin ta ya suka iya yin hakan
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wasu ma'aurata baƙar fata da farar fata sun yi iƙirarin karya tarihin kundin Guiness na lokaci mafi tsawo da ma'aurata suka kwashe suna yin waya bayan sun yi sa'o'i 101 suna magana a waya ba tare da sun tsaya ba
Ma'auratan waɗanda suka haɗa da wani ɗan Najeriya mai suna Cyprian da wata baturiya mai suna Sarah, sun sanar da hakan ne a shafinsu na TikTok.
Da su ke nuna shaidar yin kiran na su, ma'auratan sun kira shi da sunan 'call-a-thon' inda suka yi nuni da cewa ya ɗauki tsawon sa'o'i 101 da mintuna 15 da daƙiƙa 40 wanda hakan na nufin kwana huɗu da sa'o'i biyar.
Ba a sani ba dai cewa ko kiran da suka yi sun yi ne domin shiga cikin kundin tarihi na Guinness.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ma'auratan dai sun bayyana cewa soyayyar nesa ba ta waɗanda basu da ƙarfin zuciya ba ce.
A cewar kundin Guinness, tarihin kiran da aka daɗe ana yi a waya, wasu mutum huɗu ne su ke riƙe da shi. Na farko Latvians Kristaps Štãls wanda aka haɗa shiɓda Patriks Zvaigzne, sai Leonids Romanovs wanda aka haɗa shi da Tatjana Fjodorova.
Su dukansu sun yi magana har ta sa'o'i 54 da mintuna huɗu inda suka yi magana kan batutuwa da dama.
Hazikin Matashi Dan Najeriya Ya Sace Zuciyar Kyakkyawar Budurwa Cikin Minti 5, Hirarsu Ta Bada Mamaki
Hotunan Wata Dattijuwa Sun Janyo Cece-Kuce
A wani labarin kuma, wata dattijuwa ta bayar da mamaki sosai a yanar gizo bayan bayyanar hotunanta. Dattijuwar dai tana kama da matashiyar budurwa.
Mutane sun yi ta mamaki da suka ji cewa tana da ƴaƴa bakwai da jikoki biyar, duk kuwa kamanninta sun nuna akwai sauran jini a jikinta.
Asali: Legit.ng