Kundin Bajinta Na Guinness: Wani Dalibi Ya Dukufa Wajen Rubutu Har Na Tsawon Mako 1 Don Kafa Tarihi
- Wani matashi mai suna Daniel Aiguokhian ya shirya tsaf don kafa tarihi a kundin bajinta na Guinness
- Matashin wanda dalibi ne a jami'ar Calabar zai fara rubutu har tsawon mako guda wanda zai shafe sa'o'i 168
- Daniel zai shafe kwanaki bakwai da sa'o'i 20 yana rubutu yayin da zai samu hutun sa'o'i bakwai da mintuna 10 kacal
Wani dalibin jami'ar Calabar mai suna Daniel Aiguokhian ya shirya kafa sabon tarihin kundin bajinta na Guinness wanda yafi kowa dadewa yana rubutu.
Dalibin ya himmatu don ganin ya fi kowa dadewa yana rubutu don kafa sabon tarihi a kundin Guinness, wanda rubutun zai kai sa'o'i 168.
Daniel zai shafe kwanaki bakwai da sa'o'i 20 yana rubutu yayin da zai samu hutun sa'o'i bakwai da mintuna 10 kacal.
Dalibin zai rubuta littattafai biyu a kullum
Yayin aikin, Daniel ya rubuta littattafai guda biyu a kowace rana, inda zai yi rubutun da hannunsa da kuma farar takarda.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dalibin zai bar mu'amala da wayarsa na tsawon lokaci, yayin da wasu mutane za su ke kula da kafafen sadarwa da yake amfani da su.
Sannan za a nuna bajintar dalibin kai tsaye a kafafen sada zumunta kamar Twitter da Facebook da Instagram da kuma YouTube.
Mutane da dama sun mai da martani kamar yadda Legit.ng ta tattaro:
Mc Sammv-b:
"Ya kamata kundin tarihi na Guinness su ba wa 'yan Najeriya kyauta da suka wuce mulkin Buhari lafiya. Ba abun da yafi haka jarumta."
Capable Ofemtv:
“Dukkanmu mun kafa tarihi a duniya, kawai dai mu ba a nuna mu ne."
Agboola Ayomide:
“Tun da 'yan Najeriya suka samu wannan littafin kambun Guinness, sai sun yaga shi nan ba da jimawa ba."
Celia Adinya:
“Ya na so ya rubuta dukkan tsiyar da jami'ar Calabar suke kunsa masa ne."
Hilda Baci: Abubuwa 6 Da Mutum Zai Amfana Da Su Bayan Kafa Tarihi A Kundin Bajinta Na Guinness
A wani labarin, wata matashiya 'yar Najeriya mai suna Hilda Bachi ta kafa tarihi a kundin bajinta na Guinness.
Budurwar ta shafe sa'o'i 100 tana girki ba tare da tsayawa ba, wanda hakan ya bata damar kafa tarihin.
Hilda wanda asalin 'yar jihar Akwa Ibom ta fi kowa dadewa tana girki a duniya kmar yadda kamfanin ya fada.
Asali: Legit.ng