"Ni Na Fara Cewa Ina Son Shi": Dattijuwa 'Yar Shekara 60 Mai Soyayya Da Matashi Dan Shekara 27 Ta Bayyana
- Wata mata mai shekara 60 a duniya, Yusta Lucas, ta shirya yin komai domin kare masoyinta mai shekara 27 wanda za su yi aure kwanan nan
- Yusta tana matuƙar son masoyin nata inda ta ke masa kallon mijinta inda ta riƙa nuna irin maitar da ta ke masa a fili a wata tattaunawa
- Matar ta yi nuni da cewa a wajen masoyinta, ita ce mace wacce ta fi kowacce kyau kuma bata tsoron komai ko wani
Wata mata mai shekara 60 a duniya, Yusta Lucas, ta faɗa cikin kogin ƙaunar rabin ranta mai shekara 27 a duniya, inda su ke ta shirye-shiryen yin aurensu.
A wata tattaunawa da Mbengo TV, dattijuwar matar Yusta Lucas ta bayyana cewa ta taɓa aure a baya amma mijinta na farko ya kwanta dama.
"Ta Hanyar Kyakkyawar Niyya": Matashiyar Budurwa Ta Fice Daga Makaranta, Ta Samu N2.1bn a Cikin Wata Shida
Ta yi nuni da cewa ta yi rayuwar kaɗaici har ta shekara uku lokacin da mijinta ya mutu, kuma ta haifi yara a auren da ta yi a baya.
Yusta ta bayyana cewa marigayin mijinta ya bar dukiya mai tarin yawa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A kalamanta:
"Lokacin da mijina ya kwanta dama, ya bar dukiya mai tarin yawa. Bayan haka ni da mijin da zan aura mun haɗu a ɗaya daga cikin shagunan da mijina ya mutu ya bari domin yana kawo min ziyara nima ina kai masa."
Dattijuwa ta fara cewa tana son matashin
Ta bayyana cewa ita ce ta fara cewa tana son matashin saboda yana matuƙar burgeta.
"Ni ce na fara cewa ina son shi (Nilimteka). Yana zuwa shagona ina ba shi abinci. Zan dafa masa abinci na ajiye a wani wajen ta yadda idan ya zo zai ɗauka." A cewarta
'Babu Macen Da Za Ta Ciyarda Iyali Na Wata Daya, Ba Tare Da Cin Zarafin Miji Ba,' Bidiyon Wata Budurwa Ya Tada Kura A Intanet
Matashin ya bayyana cewa shi a wajen shi baya jin cewa Yusra ta kwana biyu ko ta yi masa tsufa.
A kalamansa:
"Ina mata kallon budurwa sharaf ƴar shekara 20. Duk wani abu da mace ta ke da shi tana da shi. Ƴan mata sa'anni na sun cika taurin kai ni kuma bani da lokacin da zan biye musu."
"Ba zan iya ɓata lokaci a kansu ba akwai abubuwan da na mayar da hankali akai. A rayuwa ka nemi abinda zai sanya ka farin ciki."
Masoyan biyu dai sun shirya yin wuff da juna sannan sun tabbatar da ba za su taɓa rabuwa da juna ba.
Wata Budurwa Ta Bude Wa Mata Aiki
A wani labarin na daban kuma, wata budurwa ta bayyana wani sirri na matan daɓke ɗaukar ragamar gidajensu a maimakon mazajensu.
Budurwar ta bayyana cewa babu matar da za ta riƙa ciyarwa a gidan mijinta ba tare da jikin mijin ya gaya masa ba. Ta bayyana duk macen da ta ke haka sai ta ci zarafinsa daga baya.
Asali: Legit.ng