Inda Ranka: ’Yar Najeriya Ta Yi Dabara a Kasar Turai, Ta Kama Siyar da Dafaffen Abincin Najeriya

Inda Ranka: ’Yar Najeriya Ta Yi Dabara a Kasar Turai, Ta Kama Siyar da Dafaffen Abincin Najeriya

  • Wani faifan bidiyo da ya yadu bayan an gano wata daliba na siyar da shinkafa a cikin aji a Burtaniya
  • Wadda ta wallafa faifan bidiyon ta bayyana cewa ba harkar kasuwanci ba ne kawai sun saka ta ne
  • Bidiyon ya jawo cece-kuce daga masu ta'ammali da kafar sada zumunta inda wasu suka kushe abin

An gano wata matashiya 'yar Najeriya a wani faifan bidiyo ta na siyar da abinci a cikin aji ga dalibai a kasar Birtaniya.

Daya daga cikin daliban da ta yada faifan bidiyon ta ce kashi 90% daga cikin daliban 'yan Najeriya ne, inda ta ce har shinkafa suke siyarwa.

'Yar Najeriya yayin da ke siyar da shinkafa a kasar Turai
'Yar Najeriya Yayin da Take Siyar da Shinkafa A Cikin Aji. Hoto: @yhuudee.
Asali: TikTok

A faifan bidiyon, mai siyar da abincin ta na raba abincin yayin da wani kuma a gefe yana mika mata kudi madadin abincin da ake karba.

Kara karanta wannan

"Ki Bar Bawan Allah Ya Huta": Bidiyon Wata Budurwa Da Saurayinta Suna Jin Daɗi a Dakin 'Hotel' Ya Girgiza Mutane

'Yar Najeriya ta siyar da abincin ne a Jami'ar Portsmouth da ke Burtaniya

Legit.ng ta tattaro cewa wannan lamari ya faru ne a jami'ar Portsmouth da ke Burtaniya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A can wani bangare an ji wata murya ta na cewa akwai shinkafa idan da mai siya.

Faifan bidiyon ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta inda mutane da dama suka tofa albarkacin bakinsu.

Mutane sun gargadi budurwar ta cire wannan faifan bidiyo don gudun rikici

Wasu mutane sun gargadi wadda ta wallafa bidiyon cewa ta yi gaggawar goge bidiyon kada ya jawo rigima.

Yayin da wasu kuma suka yabi yadda 'yan Najeriya ke son harkan kasuwanci a ko ina suke.

Wadda ta wallafa bidiyon ta mai da martani ga wadanda suka tofa albarkacin bakinsu da cewa:

"Ba kasuwanci ba ne, hhh kawai mun saka ta ne ta yi don mu biya ta..hhh ."

Kara karanta wannan

Ziyara Zuwa Kano: Shigar Da Jarumar Fim Nancy Isime Ta Yi Ya Bada Mamaki, Ana Ta Tafka Mahawara

Ku kalli bidiyon a kasa:

Mutanen masu ta'ammali da kafar sada zumunta sun tofa albarkacin bakinsu:

user4367585667:

"Wannan ai shinkafa ce da aka sauya mata launi, ba soyayyar shinkafa ba ce, ina iya ganin kananan karas guda biyu."

Vincent:

"Makarantarmu ba za ta taba yin haka ba, masu digiri na biyu ko 40 ba su kai ba a bara."

Micheal (temidayo titilola):

"Ku taimaka ku cire bidiyon nan, hakan ya sabawa dokar da ta ba ku daman zama a can.

Veeveeyan:

"Ba komai ne da ya faru a jami'a za a saka a kafafen sada zumunta ba, kuna zubar wa wannan jami'a kima."

Squidward Tentacles:

"Wannan ba ko ina ba ne sai jami'ar Portsmouth.

Hairbyberyl:

"Ina ma ace wani zai siyar da wannan a makarantarmu, muna fama da "yunwa a makaranta."

ButaFly:

"Me yasa nake ta kallon wannan bidiyon, har shinkafar ta shiga baki na .

Kara karanta wannan

"Abin Da Ciwo": Wata Da Ke Saudiyya Ta Yi Kuka Ganin Halin Da Yayanta Ke Ciki Duk Da Tana Turo Kudi Duk Wata

Wotzerface:

"Ina son shinkafa dafa duka.

"Abin Da Ciwo": Wata Da Ke Saudiyya Ta Yi Kuka Ganin Halin Da Yayanta Ke Ciki Duk Da Tana Turo Kudi Duk Wata

A wani labarin, wata mata da ke rayuwa a Saudiyya ta shiga yanayi bayan ganin yadda 'yarta ta kasance a gida.

Matar ta ce kullum wata ta na turo makudan kudade don kula da yaranta amma ba ta yi tsammanin ganin 'yar haka ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.