Na Siyar da Jaririna Don Magance Matsalolin Iyali, Cewar Wata Mata a Yayin Da Ta Shiga Hannun Hukuma
- Yan sanda a Legas sun cafke wata mata mai matsakaitan shekaru bisa tuhumarta da yunƙurin siyar da jaririnta kan kudi N300,000
- Matar mai suna Maria ta ce mijinta bai damu da kula jaririn ba sannan kuma ta na so ta magance wasu matsaloli na gida da suka addabeta
- Yan sandan sun kuma yi nasarar damƙe wacce ta shiga tsakani wajen gudanar da cinikin jaririn
Legas - Rundunar ‘yan sanda jihar Legas ta cafke wata mata mai shekaru 26 mai suna Maria Ahmadu a lokacin da take ƙoƙarin siyar da jaririnta ɗan watanni biyu a kan kuɗaɗe N300,000.
Haka kuma, sun kama wata mata yar kimanin shekaru 25, mai suna Oge Okolie, wacce suka bayyana a matsayin mai shiga tsakani, tare da mahaifiyar jaririn da aka yi yunƙurin siyarwa.
Buƙatar kuɗi ce ta sanya ta hakan
Sai dai a rahoton Daily Trust, 'yan sandan sun bayyana cewa ba su samu nasarar damƙe mai siyan jaririn ba, saboda ya riga da ya cika wandonsa da iska.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An bayyana cewa Okolie ta ɗauki jaririn da zimmar ta kai wa mai siye, wanda a lokacin ne jami'an suka yi nasarar damƙeta bayan ta shiga wata mota ƙirar bus a unguwar Oshodi da ke Legas.
Da take bayar da bayani a hannun hukuma, mahaifiyar jaririn ta bayyana cewa tana cikin tsananin buƙatar kuɗi domin ta magance wata matsala ta gida.
Mahaifinsa bai damu dashi ba
Sannan ta ƙara da cewa ta yanke shawarar siyar da jaririn ne tunda mahaifinsa bai damu da kula da shi ba.
A cewarta:
“Ina buƙatar kuɗin ne domin in warware matsala a cikin gida tun da mahaifin jaririn bai nuna ya damu da kula da yaron ba.”
“Oge ce ta tuntuɓi mai siyan bayan na fada mata matsalar kuɗi da nake ciki. An kama ta ne a lokacin da take kan hanyarta ta zuwa kai jaririn.”
Akan 300,000 aka yi cinikin jaririn
Mahaifiyar jaririn ta kuma shaidawa jami'an tsaron cewa N300,000 ne ta amince da siyar da jaririn na ta.
"Ban san nawa Oge ta yi ciniki da mai siyan ba, iyaka dai kawai ta faɗa min cewa za a biya ni N300,000 idan na yarda zan siyar da yaron nawa."
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Matashi ya kashewa budurwarsa dubu 500 da ya ranto a banki
Wata budurwa ta bayyana yadda saurayinta ya ciyo bashin kuɗaɗe har N500,000 daga banki sannan ya ba ta kyautar su duka, bayan da ta nemi ya nuna mata irin ƙaunar da yake yi mata.
Budurwar dai ta bayyana cewa saurayin nata ya ce ta kashe kuɗaɗen yadda ta ga dama, duk kuwa da cewa albashin dubu 40 yake ɗauka a wata.
Asali: Legit.ng