Magidanci Ya Nuna Tsala-Tsalan 'Ya'Yansa Mata 10, Bidiyon Su Ya Dauki Hankula

Magidanci Ya Nuna Tsala-Tsalan 'Ya'Yansa Mata 10, Bidiyon Su Ya Dauki Hankula

  • Wani mutum wanda ya ce Allah ya albarkace shi da ƴaƴa mata 10, ya garzaya yanar gizo domin nunawa duniya su
  • Ƴanmatan guda 10 duk sun girma, kuma an nuna su a cikin wata mota yayin da suka riƙa fitowa ɗaya bayan ɗaya lokacin da motar ta tsaya
  • Wasu daga cikin masu amfani TikTok da suka yi arba da bidiyon sun yi mamakin yadda mutum ɗaya ya samu ƴaƴa mata 10

Wani magidanci wanda ya ke da ƴaƴa mata 10, ya nuna wa duniya su a cikin wani bidiyon TikTok wanda ya yaɗu sosai.

A cikin bidiyon wanda @prince_eddy_tawa, ya sanya a TikTok, magidancin ya cika da farin ciki lokacin da ƴanmatan su ke fitowa ɗaya bayan ɗaya daga cikin mota.

Magidanci ya nuna 'ya'yansa mata 10 a cikin bidiyo
Magidancin yana da 'ya'ya 10 duk mata Hoto: TikTok/@prince_eddy_tawa
Asali: TikTok

Bidiyon ya nuna ƴanmatan sun gwamutsu su duka a cikin mota ɗaya gwanin ban dariya.

Kara karanta wannan

Dan Daudu Bobrisky Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ba Ya Son Ƙulla Wata Alaƙa Da Abokai

Bidiyon ya nuna ƴanmata 10 ƴaƴan mutum ɗaya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mahaifin ƴanmatan ya tsaya cike da jindaɗi yayin da suke saukowa, har sai da su 10 suka gama nuna fuskokin su.

Dukkanin su dai sun zama manyan ƴanmata, yayin da mutane da dama suka kira shi da cewa lallai yana da sa'a.

Ya yi ta ƙirga su ɗaya bayan ɗaya lokacin da su ke fitowa daga cikin motar har sai da aka kai kan ta 10, wacce itace ke tuƙa motar. Bidiyon ya ɗauki hankulan mutane sosai a TikTok.

Amma wasu daga cikin mutanen da suka kalli bidiyon, sun yi musun cewa babu yadda za a yi ƴanmata 10 su gwamutsu cikin mota ɗaya.

Wasu sun bayyana cewa ba shawara ba ce mai kyau ƴan gida ɗaya su taru a cikin mota ɗaya, ko da abinda ba a tsammani ka iya faruwa.

Kara karanta wannan

“Na Haɗa Kayana Na Bar Gidan": Wani Magidanci Yayi Fushi Ya Bar Matarsa Bayan Da Surukarsa Ta Dawo Gidansu

Matashi Mai Soyayya Da 'Yanmata Biyu Ya Nuna Su, Bidiyon Ya Dauki Hankula

A wani labarin na daban kuma, wani matashi ya nuna kyawawan ƴan mantansa guda biyu da ya ke kwasar ƙauna a wajen su. Matashin ya ce su duka biyun sunaatuƙar ƙaunarsa.

Matashin ya bayyana cewa soyayya da mace ɗaya lallura ce saboda shi yanzu kakarsa ta yanke saƙa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng