"Wannan Za Ta Iya Gyara Najeriya": Budurwa Mai Tallar Kwai Ta Shirya Su Tsaf Kamar Bene a Farantin Talla

"Wannan Za Ta Iya Gyara Najeriya": Budurwa Mai Tallar Kwai Ta Shirya Su Tsaf Kamar Bene a Farantin Talla

  • Wata budurwa mai siyar da ƙwai ta birge mutane sosai a TikTok saboda yadda ta jera su tsaf-tsaf akan farantin talla
  • Ta ɗauki dogon lokaci wajen jeranta ƙwayayen, ta daidaita su tare a hawa takwas wanda ya yi kama da bene
  • Mutanen da suka haɗu da matashiyar akan titi sun yi ta mamakin yadda ta iya sanyawa ƙwayayen suka tsaya a haka

Wata matashiyar budurwa mai siyar da ƙwai, ta jeranta ƙwayayenta a wata siga wacce ta ɗauki hankulan mutane sosai.

Lokacin da ta fita kan titi ɗauke da farantin da ta ke talla da shi a kanta, mutane da dama da suka hangota, sun matso kusa domin su ƙara ba idanunsu abinci.

Budurwa ta shirya kwai tsaf kamar bene a bidiyo
Mutane sun yi ta mamakin yadda ta shirya su Hoto: @davidoafri
Asali: TikTok

A cikin bidiyon wanda @davidoafri, ya sanya a TikTok, budurwar ta jeranta ƙwayayen a tare kamar yadda ake jera bululluka.

Kara karanta wannan

Buhari Na Iya Bakin Ƙoƙarinsa Wajen Magance Matsalar Hauhawar Farashi a Najeriya, Cewar Garba Shehu

Bidiyon ya nuna haziƙar mai tallar ƙwai

Yadda ta jera ƙwayayen a hawa takwas, ya sanya ya yi kama da kamar wani bene ne wanda ƙwararrun magina suka gina.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ba ƙwayayen kawai ta sanya a cikin farantin tallar ba, ta kuma yi amfani da barkono wajen maƙale ƙwayayen tare.

Ganin yadda farantin tallar ya zauna daram akan budurwar, mutane za su yi tunanin cewa zai iya faɗowa ƙwayayen su fashe, amma ita ko a jikinta saboda ta yadda ta kanta.

Mutane da dama sun yaba mata kan yadda ta yi amfani da salon ƙwarewa wajen sana'arta. Ga kaɗan daga ciki:

@Frimpomaa ya rubuta:

"Wannan matar za ta iya kula da tattalin arziƙin Ghana da Najeriya."

@S ya rubuta:

"Ta jera ƙwayayen gwanin ban sha'awa."

@Osariemen ya rubuta:

Kara karanta wannan

Labari Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Sake Kai Mummunan Hari a Abuja, Sun Sace Mutane Da Dama

"Wow wannan abin birgewa ne."

@user3501388666464 Kelly ya rubuta:

"Wannan matar za ta iya samar da kyakkyawar ƙasar Ghana."

@Priscy ta rubuta:

"Wannan matar za ta iya saita tattalin arziƙin Ghana."

@Becky bell ta rubuta:

"Wooo Allah ya albarkaci sana'arki."

’Yar Najeriya Ta Bude Buhun Shinkafa, Ta Fara Kirge Don Sanin Kwaya Nawa Ne a Ciki

A wani labarin na daban kuma, wata ƴar Najeriya ta samarwa kanta aikin yi, inda ta duƙufa ƙirga ko shinkafa guda nawa ce a cikin buhun shinkafa.

Budurwar dai ta duƙufa wannan aikin ne domin kafa tarihi a duniya. Ta kuma sha alwashin sai ta kammala wannan aikin ba tare da nuna gajiyawa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng