Kungiyar Zaurawa Ta Yi Bikin Karbar Sabbin Mambobinta, Bidiyon Ya Yadu

Kungiyar Zaurawa Ta Yi Bikin Karbar Sabbin Mambobinta, Bidiyon Ya Yadu

  • Wani faifan bidiyo da ya yadu a kafar sada zumunta ya jawo martani daga mutane da dama bayan an gano kungiyar zaurawa na biki
  • A faifan bidiyon an gano kungiyar zaurawan na bikin karbar sabbin mambobinta a Port Harcourt babban birnin jihar Rivers
  • Wanda ya wallafa faifan bidiyon a shafinsa na Twitter ya bayyana yadda suke gudanar da bikin nasu na karbar sabbin mamabobin

A wani faifan bidiyo da ya yadu a kafar sada zumunta, an gano kungiyar zaurawa suna bikin karbar sabbin mambobi don shiga kungiyar.

Wanda ya wallafa faifan bidiyon Abdullah Ayofele a shafinsa na Twitter ya ce bikin ya gudana ne a Port Harcourt babban birnin jihar Rivers.

Bidiyon zaurawa ya yadu yayin karban sabbin mambobi
Bikin kaddamar da sabbin zaurawa | Hoto: @abdullahayofel
Asali: Twitter

Ayofele ya yi rubutu a saman faifan bidiyon kamar haka:

"Wahala Wahala Wahala.

Kara karanta wannan

Rundunar ’Yan Sanda Ta Bayyana Dalilin da Yasa Suka Sanya Wa Seun Kuti Ankwa Bayan Ya Mika Kansa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Taron kungiyar zaurawa na bikin karbar sabbin mambobi yayin da suka yi wa bikin lakabi da ‘Karshen matsala’ ka yi rayuwa ba takurawa a Port Harcourt, taken kungiyar shine “Nayi, Na kara yi, kuma na gama.......hahah.”

Sannan akwai kek mai dauke da “Nayi, na kara yi kuma gama” wanda daya daga cikin matan ta dauka yayin da sauran mata suke cikin nishadi.

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu akan faifan bidyon.

Ga faifan bidiyon da aka wallafa a kasa:

Martanin mutane da dama da suka tofa albarkacin bakinsu

@arcadol:

“Abin da ubangiji ya hada wa ya isa ya raba? Bai kamata mu rinka kula da wadanda muke tare da su ba? #Aljanu.”

@gbonjunbolaO:

“Me yasa maza suke kuka duk lokacin da mata suka nemi saki? Rabuwan yafi konawa maza rai fiye da matan.”

Kara karanta wannan

Wasu Wurare 4 da Bola Tinubu Zai Iya Shan Wahala Bayan Ya Gaji Muhammadu Buhari

@GentleTLADY:

“Kayi tunanin in ‘ya’yansu suna wurin za su ce su ma wataran matansu ne anan sun hadu da iyayensu, za su kasance su kuma kaman iyayensu maza,”

@Dami4Change:

“Farin ciki kyauta ne.”

@AdebowaleShogb3:

“Tun da a Port Harcourt ne manta mallam. Wadanda kuke gani anan kadanne, da yawansu suna gidajen mazajensu amma ba zaman aure ba.”

Wata Budurwa Ta Fashe Da Kuka Bayan Shafe Makwanni 3 Babu Cinikin Ko Kwandala a Shagonta

A wani labarin, a wani faifan bidiyo da ya yadu an gano wata budurwa mai siyarda kayan kawa ta fashe da kuka saboda rashin ciniki a shago.

An nuno budurwar na zagayawa tana daukan bidiyon yayin da take kokawa da rashin ciniki a shagon na tsawon makwanni uku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.