Mutuwar Aure: Maimunatu Giwa Ta Ce Ko Jibganta Miji Ke Yi Ba Za Ta Bar Shi Ba
- Maimunatu Giwa ta bayyana cewa akwai ƙalubale sosai a zaman zawarci musamman ma ga wacce ba ta da tudun dafawa
- Ta bayyana cewa mata sukan daɗe a gida bayan mutuwar aurensu ba tare da sun samu kalar irin mijin da suke so ba
- Ta ce ba ta da burin komawa gidan tsohon mijinta saboda tana ganin cewa yanzu kamar ta wuce da ajinshi
Jihar Kano - Maimunatu Abdullahi Musa, wacce aka fi sani da Maimunatu Giwa, ta bayyana cewa idan ta yi aure ko dukanta mijin zai riƙa yi ba za ta rabu da shi ba.
Maimunatu, wacce shahararriyar mai amfani da kafar sadarwa ta Facebook ce, ta bayyana hakan ne a wata hira da ta yi da gidan rediyon Freedom da ke Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zaman gida bayan mutuwar aure ya na da ƙalubale - Maimuntau Giwa
A yayin hirar, Maimunatu ta bayyana cewa zaman gida akwai ƙalubale, a dalilin hakan ne ta shawarci duk macen da aurenta ya mutu to ta yi ƙoƙarin kama sana'a saboda ƙalubalen da za ta riƙa fuskanta a zaman gidan iyayenta.
Ta ce idan kuma ba ta da ra'ayin sana'a to tana shawartarta da ta koma makaranta, ma'ana ta ci gaba da karatu na gaba da sakandare ta yiwu ta dace da samun aiki bayan kammala karatun, wanda hakan zai yi matuƙar taimaka mata.
Ta kuma bayyana cewa yanzu idan aka saki mace takan daɗe ba ta samu wani mijin ba saboda dole sai mace ta tsaya ta tantance don gudun komawa gidan jiya.
Maimunatu ta ce idan aka zo kan maganar mutuwar aure, to dole fa kowa yana da nasa laifin. Ta ce ba za a ɗauki mutum ɗaya a tsakanin mata da miji ba a ce shi kaɗai ke da laifi.
"Ni Ba Kowa Bane Idan Ba Ki" Matashi Ya Roki Tsohuwar Budurwarsa Da Sako Mai Sosa Zuciya, Ya Fusata Samari
Ba zan iya komawa gidan miji na na da ba
Da aka tambaye ta kan cewa me zai hana a yanzu ta koma gidan tsohon mijinta sai ta kada baki ta ce:
“A ni gaskiya ba zan iya komawa gidan mijina ba, saboda kawai yanzu ina ji a raina shi ba aji na bane. Wancan ma ƙuruciya ce ta sa na aure shi da kuma mummunar ƙaddara.”
Ta ce ba ta tunanin cewa macen da aurenta ya mutu ta kama kasuwanci za ta iya komawa mijinta na baya, domin ko a cewarta kowa yana son ci gaba a rayuwa.
Maimunatu ta bayyana cewa ta ɗauki babban darasi a rayuwarta ta zaman gida kuma kullum a cikin ɗaukar darasin ta ke. Ta ƙara da cewar ko dukanta mijin da za ta aura yake ba za ta bar shi ba.
A kalaman ta:
“Ai darasin yana da girma kuma kullum a cikinshi nake. Amma kasan menene, kawai ina ji a raina yanzu idan nai aure ko duka na ya ke yi ba zan dawo ba.”
An sanya dokar rage kashe kudin aure a jihar Sokoto
A wani labarin kuma, majalisar dokokin jahar Sokoto ta yi wata sabuwar doka da za ta sa a rage yawan kashe kudi a hidimar bukukuwa da ake yi.
Dokar dai wacce 'yan majalisar suka aminta da ita ta shafi bukukuwan aure, bikin suna har ma da na kaciya.
Asali: Legit.ng