Budurwa Ta Bai Wa Masoya Shawarar Yadda Za Su Yi Aure Da Kudi N400,000 Kacal

Budurwa Ta Bai Wa Masoya Shawarar Yadda Za Su Yi Aure Da Kudi N400,000 Kacal

  • Wata budurwa a Najeriya ta bayyana yadda masoya za su iya yin aure a cikin sauki kan kudin da bai wuce N400,000 ba
  • Ta ce dole su gane cewa ba komai ne za su dauka da zafi ba musamman dakin taro ko a majami’ar da za su iya yin taronsu
  • Sannan ta ce maganar daukar hoto za su iya samun wayar tafi da gidanka ko da iPhone ce su dauki hotonansu

Wata matashiya ‘yar Najeriya, Butter Bibi ta bayyana cewa masu shirin yin aure za su iya kashe N400,000 kacal a bikinsu.

@Butter Bibi ta ce masoyan za su iya samun dakin taro na majami'a da kuma wayar tafi da gidanka ko da iPhone ce kuma su kashe abin da baifi N100,000 ba a daukan hoto.

Kara karanta wannan

Karfin Hali: Labarin Wani Matashin Da Ya Dirkawa 'Yan Mata 3 'Yan Gida Daya Ciki

yar najeriya
Aure a Najeriya, Hoto: @ButterBibi
Asali: Twitter

Ta kara da cewa basu bukatar sai sun samo jagoran taro wato MC, ko daya daga cikin abokansu ma zasu iya yi, mai kida kuma, ta basu shawara suyi amfani da wakokin da ke wayarsu.

@ButterBibi ta ce kayan sawa kuma kar ya wuce na N100,000, sannan ma’auratan za su iya amfani da motocin abokansu wurin zirga-zirga, cikin raha ta bai wa ma’auratan da kar su yi wasa da abinci a bikin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane da dama sun tofa albaracin bakinsu

andseller:

“Iyayenmu a Najeriya ba zasu yarda ba, musamman ‘yan Kudu maso Yamma.”

@mutedemotionns:

“Wannar yarinyar nake son aure, don Allah meye sunanta? Nasan za ta kula da kudade na sosai.”

@horllarmylekan:

“Ba za su bar irin wannan aure ya faru ba.”

@Surasongs:

“Kuna ta maganan shirme, in ba ku son aure kuyi na gargajiya, sai dai in ba ku son ciyar da mutane don ko abinci N400,000 ba zai siya ba.”

Kara karanta wannan

“Turo Mun N400k Ko Na Rabu Da Kai”: Matashiya Ta Yi Barazana Ga Saurayinta, Hoton Hirarsu Ya Bayyana

@EgbeahieS:

“Abokina ya kashe 15m a aurenshi, aure bashi da araha kwata kwata, ku nemi wadda ta dace ba shiririta ba.”

Budurwar Da Ke Tallan Kanta Da Hotunan Batsa Ta Tuba, Ta Mika Rayuwarta Ga Yesu

Wata budurwa da take yada hotunanta na batsa a baya ta kafar sada zumunta don jama’a su gani ta ce yanzu ta sauya rayuwarta.

A cewar budurwar, rayuwarta ta sauya tun bayan da ta rungumi tafiyar Annabi Isa a addinin kirista, kuma zata ci gaba da zama a haka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.