Arzikin Abdul Samad Rabiu Ya Karu da $600m, Ya Zama Attajiri na 3 a Fadin Afrika
- Idan za a lissafo manyan masu kudi uku da ake ji da su yanzu a Afrika, sai an kira Abdul Samad Rabiu
- ‘Dan kasuwan da aka haifa a jihar Kano a Najeriya ya ba $8.6bn baya, ya na gaban Nicky Oppenheimer
- Wadanda suka sha gaban Abdul Samad Rabiu a nahiyar su ne Aliko Dangote da Johann Rupert
Nigeria - Mutum na biyu da ya fi kowa arziki a Najeriya shi ne Abdul Samad Rabiu, yanzu ana maganar ya sha gaban Nicky Oppenheimer a adadin dukiya.
Wani rahoto da aka fitar a Nairametrics ya nuna Attajirin kasar Afrika ta Kudu, Nicky Oppenheimer ya rasa matsayinsa ga Alhaji Abdul Samad Rabiu.
Yanzu Abdul Samad Rabiu ne mutum na uku da ya fi kowa dukiya a nahiyar Afrika, ana hasasashen abin da mai kudin ya tara sun kai fam Dala biliyan 8.6.
A daidai lokacin da ake rubutun nan, arzikin ‘Dan kasuwan da aka haifa a Kano ya karu da Dala biliyan 3.7 daga shekarar bara da ya mallaki Dala biliyan 4.9.
$600m a watanni 3
Watanni uku da suka wuce Attajirin ya tara abin da ya kai Dala biliyan 8, bayan ‘yan kwanaki sai aka ji kudinsa ya karu da Dala miliyan 600 (Naira biliyan 270).
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A kaf kasashen Afrika, mutane biyu ne a gaban shugaban kamfanin BUA idan ana maganar dukiya, daga cikinsu akwai Aliko Dangote da tuni ya kerewa kowa.
Ina aka baro Johann Rupert?
Na biyu shi ne Johann Rupert na Afrika ta Kudu wanda Bloomberg ta ce ya ba Dala biliyan 11 baya. Rupert ya yi gado ne a wajen mahaifinsa, Anton R. Richemont.
Oppenheimer mai $8.4bn ya zama na hudu a jeringiyar attajiran nahiyar bakar fatan, ratar da ke tsaninsa da na uku a yanzu ba ta wuce Dala miliyan 200 ba.
A yadda arzikin mutumin Najeriyan ya ke karuwa a dare da rana, ba dole ba ne Mista Oppenheimer mai shekara 77 da haihuwa ya sake karbe wurin na sa ba.
‘Dan Afrikan ta Kudun ya yi arziki ne da kasuwancin hako gwal-gwalai da danginsa suke yi, mafi yawan kudinsa ya fito ne daga kamfanin De Beers da ya saida.
An saida hannun jarin kamfanin ga Anglo American plc a kan Dala biliyan 5.1, hakan ya yi daraja. Attajiran sun yi suna wajen matukar taimakon marasa karfi.
Abdul Samad Rabiu ne na #2 a Najeriya
Kamar yadda aka samu labari a shekarar da ta gabata, Alhaji Abdul Samad Rabiu ya zama na biyu yanzu a rukunin manya-manyan masu kudin kasar nan.
Masana su na ganin Attajirin ya kara kudi ne a sakamakon sa hannun jarin kamfaninsa a kasuwa a shekarar 2021, Mike Adenuga ne na uku a yanzu.
Asali: Legit.ng