Wani Matashi Ya Yiwa Wata Budurwa Da Ta Hana Shi Lambar Waya Wayau

Wani Matashi Ya Yiwa Wata Budurwa Da Ta Hana Shi Lambar Waya Wayau

  • Wani matashi dan Najeriya ya bayyana wani halin wayau da ya nunawa wata budurwa a yanar gizo bayan ta ƙi bashi lambar wayar ta
  • Bayan ya ga ta ƙi amincewa da buƙatar sa, sai ya tambayarta ta gaya masa sunan da take amfani da shi a Instagram, wanda ba tayi gardama ba ta bashi
  • Sai dai, lokacin da tayi ƙorafin bata da data, sai yayi mata wani tayi wanda ya sanyata yin abinda tun da farko ta ƙi yi

Wani matashi ɗan Najeriya ya burge mutane sosai a yanar gizo bisa yadda yayi amfani da hikima wajen samun lambar wayar wata budurwa, bayan da farko ta hana shi.

A hirar ta su wacce aka sanya a Twitter, wani mai amfani sunan @UJCR_ a Twitter, ya nemi budurwar da ta bashi lambar WhatsApp ɗin ta, amma sai ta ƙi inda take cewa bata son yin hakan.

Kara karanta wannan

Kyakkyawar Baturiya Ta Kai Saurayinta Ɗan Najeriya Ganin Surukai, Yadda Suka Tarɓe Shi Ya Ɗaure Kai

Matashi
Wani Matashi Ya Yiwa Wata Budurwa Da Ta Hana Shi Lambar Waya Wayau Hoto: Twitter/@UJCR
Asali: UGC

Bai damu ba, sai ya buƙaci ta gaya masa sunan da take amfani da shi a Instagram domin su ƙulla ƙawance a can.

Lokacin da ya nemi tayi magana a Instagram, sao budurwar ta kawo uzurin cewa bata da data, hakan ya sanya ya ha dama ta samu wacce zai yi mata wasa da hankali.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya gaya mata ta bayar da lambar wayar ta da layin da take amfani da shi ta yadda zai tura mata data har (10GB).

Ba tayi wata-wata ba ta tura masa lambar wayar wacce a baya tayi ta ɓoyewa. Hakan ya sanya matashin mamaki matuƙa.

Mutane da dama sun yabawa matashin saboda yadda ya sanya basira wajen neman abinda yake so, yayin da suka yi ta yiwa budurwar dariya.

Ga kaɗan daga ciki:

IamDukeilorin ya rubuta:

"Irin wannan dubarar na yiwa wata wata budurwa. Ta ƙi ta bani lambar wayar ta kawai sai nace ta bani lambar akawun ɗin ta na Opay. Sauran labari ne mai dadin ji."

Kara karanta wannan

Bidiyon Matashi Mara Hannuwa Mai Rubutu Da Ƙafarsa Cikin Sauri Ya Ɗauki Hankula Sosai

@imaeight ya ributa:

"Wato ta saki baki za a turo mata data."

Kyakkyawar Baturiya Ta Kai Saurayinta Ɗan Najeriya Ganin Surukai

A wani laabarin na daban kuma, wata kyakkyawar baturiya ta garzaya da saurayin ta zuwa gidan su domin gayar da surukai.

Kyakkyawar baturiyar da farko dai ta ji tsoron wace irin tarba iyayen ta za su yiwa saurayin nata ɗan Najeriya, sai dai suna zuwa gidan sai gabaɗaya zullumin ta ya kau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel