Abin Mamaki: Bidiyon Yadda Wata Budurwa Ke Sarrafa Ƙafafun Ta Ya Ɗauki Hankula Sosai
- Wani bidiyo da ya yaɗu a TikTok ya nuna yadda wata budurwa tayi amfani da ƙafar ta wajen ɓare ayaba
- Budurwar wacce bata da hannuwa ta zauna kan kujera sannan tayi amfani da ƙafafun ta wajen ɗaukar ayabar daga cikin kwando
- Bidiyon yadda budurwar sarrafa ƙafafun ta ya ɗauki hankula sosai, inda mutane suka yi ta sharhi a kan sa
Wani ɗan gajeran bidiyo wanda ya yaɗu a TikTok ya nuna wata matashiyar budurwa na amfani da ƙafafun ta wajen ɓare ayaba cikin ƙwarewa.
Dalilin da ya sanya take amfani da ƙafafun ta shine hannayen ta ƴan ƙanana ne inda da ƙyar ake iya ganin su a cikin rigarta.
A cikin bidiyon wanda @marko_dejana, ta sanya, an nuna budurwar zaune akan wata kujera mai kyau. Bidiyon ya kuma nuna wani ɗan ƙaramin kwando cike da tuffa da ayaba.
Bidiyon ya nuna yadda budurwar ta miƙar da ƙafafun ta daga kan kujerar sannan ciki natsuwa ta ɗauko ayaba daga cikin kwandon.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daga nan sai tayi amfani da ƙafarta ta dama ta ciro ayaba ɗaya daga cikin sauran tarin. Tayi amfani da ƙafar ta wajen kai ayabar ɗan ƙaramin hannun ta na dama domin cire kan.
Yadda ta cigaba da ɓare ayabar sannan ta kai ta baki da ƙafarta ta fara ci yaba mutane da dama mamaki.
Bidiyon ya ɗauki hankula sosai
Bidiyon ya ɗauki hankula sosai a tsakanin masu amfani da TikTok, waɗanda suka yi tayin tambayoyi ga budurwar wacce alamu suka nuna kamar tana da juna biyu.
Ga kaɗan daga ciki:
@Barb James ya rubuta:
"Ke ta daban ce kyakkyawa."
@donnavalvano ya rubuta:
"Allah yayi albarka, ba zan iya yin wannan haƙurin ba."
@Patty Barcia132 ta rubuta:
"Shin yanzu kina shan wuya wajen yadda kike gudanar da abubuwan ki da alamu suka nuna kamar kina da juna biyu?"
@Yearsummer ta rubuta:
"Waye yake taimaka miki idan kina so kije banɗaki? Misali idan kina son kiyi bahaya?"
Ango Yayi Abin a Yaba, Ya Ziyarci Abokinsa a Gadon Asibiti Wanda Bai Samu Zuwa Bikin Sa Ba
A wani labarin na daban, wani ango yayi abin a zo a yaba bayan ya ziyarci abokin sa a asibiti ana gama ɗaura masa aure.
Abokin dai rashin lafiya ya kama shi, shiyasa bai samu halartar ɗaurin auren ba.
Asali: Legit.ng