"Ba Zan Ƙara Yin Zaɓe Ba" Matashi Ɗan Najeriya Ya Fusata, Ya Jefa Katin Zaɓensa Cikin Bola

"Ba Zan Ƙara Yin Zaɓe Ba" Matashi Ɗan Najeriya Ya Fusata, Ya Jefa Katin Zaɓensa Cikin Bola

  • Wani matashi ɗan Najeriya ya bayar da mamaki bayan ya jefar da katin zaɓen sa cikin i da ake ƙona bola
  • Matashin wanda sakamakon zaɓen shubagan ƙasa bai yi masa daɗi ba, yasha alwashin ba zai ƙara yin zaɓe ba
  • Bidiyon ya janyo cece-kuce a yanar gizo inda wasu suka yi ta ƙoƙarin nuna masa cewa ya tafka kuskure

Wani matashi ɗan Najeriya wanda sakamakon zaɓen shugaban ƙasa bai yiwa daɗi ba, ya jefar da katin zaɓen sa a bola.

Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), ya sanar da cewa tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, shine ya lashe zaɓe a ranar Laraba, 1 ga watan Maris 2023 a birnin tarayya Abuja.

Katin Zaɓe
"Ba Zan Ƙara Yin Zaɓe Ba" Matashi Ɗan Najeriya Ya Fusata, Ya Jefa Katin Zaɓensa Cikin Bola Hoto: TikTok/kalakutaways
Asali: UGC

Mutane da dama akwai yadda suka ji sanarwar. Matashin yana ɗaya daga cikin waɗanda ba su ji daɗin abinda INEC ta sanar ba.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2023: Jigon PDP Yayi Muhimmin Kira Ga Atiku Kan Ya Haƙura Ya Yarda Da Sakamakon Zaɓe

A wani bidiyon TikTok, matashin ya nuna katin zaɓen sa na din-din-din (PVC) yayin da yake tafiya zuwa inda ake ƙona bola. Yana ƙarasawa kusa da wajen kawai sai ya jefa katin zaɓen a ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rubutun da yayi a jikin bidiyon ya bayyana cewa ba zai ƙara yin zaɓe ba. Wani rubutun kuma ya bayyana cewa:

"Jefar da katin zaɓe na a wajen ƙona bola mafi kusa."

Lokacin da wani ya tuna masa da katin zaɓen sa sai yace ai yana da ƙatin shaidar zama ɗan ƙasa (NIN)

"Ba komai ina NIN don haka ba damuwa" Inji shi

Your Boo said ya rubuta:

"Kada ka manta dai ka tabbatar ka ɗauko abin ka."

Whiskey mistress ta rubuta:

"Za a sake zaɓe. Ka taimaka ka adana shi."

iyiola1233 ta rubuta:

"Kai kawai saboda zaɓe kake ganin kana buƙatar katin zaɓe ko? Lol."

Kara karanta wannan

Zaɓen 2023: Wasu Abubuwa 5 Da Suka Taimaka Wajen Samun Rashin Nasarar Rabiu Kwankwaso

user3545147050424 ya rubuta:

"A sake zaɓe ko kada a sake, Obi ba zai taɓa nasara ba, ya fiye musu su je can su kafa Biafra ɗin su, da ina goyon bayan Obi amma yanzu na ga yadda Inyamurai ke da son kai da nuna bambanci.

Her majesty ta rubuta:

"Kada ka jefar tukunna, wasan bai ƙare ba."

Peter Obi Ya Yi Magana a Karon Farko Bayan Tinubu Ya Lashe Zabe

Ɗan takarar shugabam ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, yayi magana kan kayen da yasha a hannun Tinubu.

Peter Obi yayi alƙwarin yin wani abu ɗaya rak.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng