Yadda ‘Yan ‘Yahoo Suka Damfari Tsohuwa, Suka Sace Duka Dukiyar da ta Mallaka

Yadda ‘Yan ‘Yahoo Suka Damfari Tsohuwa, Suka Sace Duka Dukiyar da ta Mallaka

  • Oladotun Ogunsanya ya bada labarin cewa ‘Yan damfara sun yaudari kakarsa, sun sace mata kudi
  • Da yake magana a Twitter, Dr. Ogunsanya ya ce ‘Yan Yahoo sun sulale N800, 000 a cikin asusun ta
  • Wannan mutumi yake cewa da aka je bankin da aka sace kudin, ba su iya dawo da kudin tsohuwar ba

Lagos - Wani Bawan Allah mai suna Dr. Oladotun Ogunsanya ya bada labarin yadda wasu da ake zargin cewa ‘yan damfara ne suka damfari kakarsa.

Dr. Oladotun Ogunsanya ya yi amfani da shafinsa na Twitter ya ce wasu miyagu sun sace N800, 000 daga asusun kakarsu mai shekaru 80 da haihuwa.

"Wannan kaka ta ce, ‘yar shekara 80 wanda duka abin da ta tara kusan N800, 000 suka fice daga cikin akawun din bankin ta.

Kara karanta wannan

Sabbin Naira: Na kusa da Tinubu ya tona asiri, gwamnan CBN na da mugun nufi kan 'yan Najeriya

Wannan ya faru ne a jiya (ranar Lahadi) da kusan karfe 06:12 na yamma bayan wani ya kira ta da sunan dillalin bankin Polaris.
Na reshen Ikorodu da ta karbi katin ATM. Jim kadan bayan gama wayan da ya yi yunkurin tantance ta, sai ga sakonnin cire kudi.
Daga nan sai aka kira ni daga wurin aiki, na zo wurinta a Epe saboda yanayin lafiyarta, nayi nawa binciken kan abin da ya faru.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohuwa
'Yar tsohuwar da aka damfara @dee_dorwiz
Asali: Twitter
Babu abin da na iya, sai dai rusa kuka. Wannan mata ce da aka aiko mata da kudin fanshonta kwanaki hudu da suka wuce.

- Oladotun Ogunsanya

Banki ba su iya yin komai ba

A labarin da ya bada, Likitan dabbobin ya ce da aka je reshen bankin da abin da ya faru a Epe, babu abin da ma’aikatan suka iya yi sai cewa a canza kati.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama ainihin mutanen da ke boye sabbin kudi, suna siyarwa a boye a Arewa

Oladotun Ogunsanya yake cewa ma’aikatan bankin ba suyi alkawarin za su dawo da kudin ba.

Hukumar FCCPC ta samu labarin martanin da bankin Polaris suka bada, suka bayyana cewa su na sa ran za ayi gaggawar daukar matakin da ya dace.

FCCPC ita ce hukumar gwamnatin tarayya da ke kula da hakkokin abokan cinikin kamfanoni.

Kamfanin Pay Stack da aka yi amfani da su sun bukaci Ogunsanya ya aika masu da bayanan asusun bankin da aka yi amfani da shi domin a binciki lamarin.

Ku na da labarin cewa ‘Yan fashi sun shiga shagon POS a garin Zaki da ke jihar Bauchi, su na neman sababbin kudi, sun yi harbe-harbe, sun sace N7m.

‘Yan Sanda sun ce za a cigaba da bakin kokari wajen cafke wadanda suka yi wannan danyen aikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng