Masu Kudi 3 Rak, Sun Zarce ‘Yan Najeriya Miliyan 83 a Dunkule Wajen Yawan Dukiya

Masu Kudi 3 Rak, Sun Zarce ‘Yan Najeriya Miliyan 83 a Dunkule Wajen Yawan Dukiya

  • Manyan Attajiran Duniya su na ta kara arziki yayin da marasa hali suke kara rungumar talauci
  • Rahoton ‘Davos 2023 Inequality Report’ ya nuna yadda masu kudi suke kara yi wa talaka fintinkau
  • Kudin da manyan masu kudin Najeriya suka tara, ya zarce abin da mutum miliyan 80 suke da shi

Abuja - Idan za a tara dukiyar mutane miliyan 83 a Najeriya, Attajirai uku kurum da ake ji da su, sun sha gaban wadannan tulin jama’a a yawan kudi.

Wani rahoto mai suna Davos 2023 Inequality Report’ da aka fitar ranar Litinin dinnan a garin Abuja, shi ya tabbatar da wannan bayani.

Shugaban Oxfam a Najeriya, Dr. Vincent Ahonsi ya gabatar da rahoton nan a daidai lokacin da ake shirin yin babban taron Duniya a Davos Switzerland.

Kara karanta wannan

A kalla Rayuka 11 ne Suka Salwanta a Wasu Hadururruka Daban-Daban a Niger

Mataimakiyar darektan sashen kula da kasafi ta Oxfam, Regina Afiemo ta wakilci Dr. Vincent Ahonsi wajen gabatar da rahoton a babban birnin Abuja.

Akwai bukatar a karawa Attajirai haraji

Sauran wadanda ke wajen su ne shugaban CODE, Hamza Lawal da Kenneth Akpan sai Henry Ushie mai jagorantar makamanciyar wannan kungiya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wadanda suka gabatar da rahoton sun hadu a kan cewa dole ne a lafta haraji a kan attajiran Duniya domin rage irin rashin adalcin da ake samu a yau.

Masu Kudi
Wasu daga cikin masu kudin Najeriya Hoto: www.bbc.com
Source: UGC

A shekarun bayan nan, an ce rabin dukiyar Duniya ta na hannun manyan attajiran da ake da su, alhali dinbin mutane su na rayuwa a talauci.

Binciken da aka yi ya nuna arzikin masu kudin Duniya yana karuwa da $2.7bn a kowace rana.

Da a ce wadannan masu kudi za su biya harajin 5%, za a iya tashi da $1.7trn a duk shekara, kudin da za su yi wa mutane biliyan biyu maganin talauci.

Kudin Najeriya su na hannun tsiraru

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

Attajirai 83 da ke kasar nan suka tashi da fiye da 60% na duka Dala tiriliyan 42 da aka samu a Najeriya daga shekarar 2020 zuwa yau.

A gida Najeriya akwai mutane 6,355 da suka mallaki fiye da Dala miliyan 5, abin da hakan yake nufi shi ne arzikinsu ya fi na mutum miliyan 107 a dunkule.

Za a kama Gwamnan CBN?

An ji labari cewa wasu fitattun Lauyoyi da ake ji da su sun aika wasika zuwa ga Ministan shari’a, Abubakar Malami a kan batun cafke Gwamnan CBN.

Lauyoyin da suka aikawa AGF wasika su ne: Adetokunbo Kayode, Oba Maduabuchi, Emeka Ozoani, M.M Nurudeen, Abdul Mohammed, da Emeka Obegolu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng