Attajiri Dahiru Mangal: Tarihin Rayuwa, Iyali, Ilimi, Arzikinsa da Sauran Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani

Attajiri Dahiru Mangal: Tarihin Rayuwa, Iyali, Ilimi, Arzikinsa da Sauran Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani

Ɗahiru Mangal, fitaccen ɗan kasuwa kuma Attajirin mai dukiya da ta kai biliyoyin daloli kuma ɗaya daga cikin Attajiran masu kuɗi 10 a Najeriya, mun haɗa muku abubuwan da ya dace ku sani game da shi.

Katsina - Dahiru Barau Mangal, fitaccen ɗan kasuwa ne ɗan asalin Najeriya, ya kafa kamfanin sufurin jiragen sama na Max Air a shekarar 2008, kamar yadda Newwire ta tattaro.

Mangal, mamallakin Max Air, kamfanin sufurin jiragen sama da ke jan ragamar sufuri a cikin gida da ƙasa da ƙasa, ya zuba hannun jari a wasu wuraren da suka haɗa da tafiye-tafiye, Mai da Gas, da gine-gine.

Dahiru Mangal.
Attajiri Dahiru Mangal: Tarihin Rayuwa, Iyali, Ilimi, Arzikinsa da Sauran Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani Hoto: newswirengr
Asali: UGC

Matar aure da 'ya'ya

Kasancewarsa Musulmi, Mangal yana da aure kuma Allah ya albarkace shi da samun ƴaƴa da dama. A shekarar 2010 an zargi Attajirin da haihuwa kafin shafa fatiha.

Kara karanta wannan

2023: Atiku da Tinubu Sun Kara Shiri, Sun Yi Sabbin Naɗe-Naɗe a Kwamitin Yakin Neman Zabe

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An haifi Ɗahiru Mangal a jihar Katsina a gidan Alhaji Barau Mangal. Ya taso tare da ƴan uwansa, Alhaji Bashir Barau Mangal, Alhaji Hamza Barau Mangal, Hajiya Zulai Barau Mangal, Hajiya Yar Goje da mahaifiyarsa, Hajiya Murjanatu Barau Mangal a Katsina.

Mangal ya fara rayuwar sana'arsa ne da aikin Direban babban Motar dakon kaya kafin daga bisani Allah ya buɗa masa ya sayi tashi Motar domin yin haya.

Farkon rayuwarsa

Mangal ya taso da sa'a a farkon rayuwarsa daga jinsin Barau Tukur da ke Anguwar Masanawa Quaters a kwaryar birnin Katsina, ya halarci makarantar Firamare Gafai daga 1960-1971 daga bisani ya zarce Katsina Arabic Teachers’ College inda ya kammala a 1976.

Shakaru: An haifi Ɗahiru Mangal a ranar 3 ga watan Agusta, 1957, shekara 65 kenan da suka wuce.

Tarihin Kasuwancinsa

Kara karanta wannan

'Ramuwar Gayya Muka Yi': Kotu Ta Yanke Wa Wasu Makiyaya Uku Hukunci Kan Ƙone Gonar Gyaɗa Ta Miliyan N1.5m

Mangal shahararren ɗan kasuwa ne wanda ke jan zarensa kuma mamallakin AFDIN Group (Nigeria) Limited, kamfanin da ke kula da kasuwancinsa da suka haɗa da Max Air, Kamfanin gine-gine AFDIN Construction Company, Manasawa Oil, Mangal Oil, da Manasawa Enterprises.

Bayanai sun nuna cewa tauraruwan Mangal ta haska ne daga irin kyakkyawar alaƙarasa da gwamnatin jihar Katsina tun tale-tale.

Alaƙarsa da gwamnan mulkin soja, Kanal Yahaya Madaki, Kaftin ɗin sojin ruwa, Emmanuel Acholonu da mulkin farar hula na Saidu Barda a 1990 sun fito da shi duniya inda ya samu kwangila a gwamnatoci.

Wannan ya ƙara ba shi damar jefa kafarsa cikin harkokin da suka shafi siyasa kuma mafi yawan dukiyarsa tana da alaƙa da abinda ya shafi siyasa kuma ya zuba jari saosai a jam'iyyar PDP, wacce ta mulki ƙasar nan da jihar Katsina tun 1999.

Osinbajo da Ɗahiru Mangal.
Attajiri Dahiru Mangal: Tarihin Rayuwa, Iyali, Ilimi, Arzikinsa da Sauran Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani Hoto: newswire
Asali: UGC

Ɗahiru Mangal ya ƙasance shugaban kamfanin MRS Oil Nigeria Plc tun 20 ga watan Maris, 2009 kuma shi ne ciyaman, cikakken shugaban kamfanin sufuri na Max Air Limited da Katsina Dyeing and Printing Textiles Limited.

Kara karanta wannan

Komai Ya Yi Farko: Gwamnan Arewa Ya Zubar Da Hawaye Yayin Gabatar da Kasafin Kudi Na Karshe

Haka nan Mangal ya kasance babban Daraktan kamfanin tafiye tafiye na Massanawa Travel & Tours da dai sauran su.

Hanyoyin samun kuɗinsa

Ɗahiru Mangal shi ne mamallakin Max Air kamar yadda muka faɗa a sama, yana da hannun jari a wasu kasuwancin da suka haɗa da tafiye-tafiye, gine-gine, Mai da gas,.

Fitaccen Attajirin yana da hannun jari mafi tsoka a kamfanin mai na Ondo Plc, inda ya samu saɓani da jagororin kamfanin har ta kai ga dakatar da hada-hadar Ondo a Legas da kasuwar canji ta Johannesburg.

Taƙaddamar ta kunno ne a 2017 lokacin da Mangal da wani mutumi da suke jan ragamar Shell suka rubuta korafi ga hukumar tsaron hada-hadar canji, wanda ya yi sanadin hukumar ta gudanar da bincike.

Sai dai an shawo kan rikicin bayan sa bakin Sarkin Kano a wancan lokacin, Sanusi Lamiɗo, a watan Janairu, 2018.

Gina Kamfanin Siminti a Kogi

Kara karanta wannan

Wike Zai Koma Bayan Tinubu? Gaskiya Ta Fito Yayin da Gwamnan APC Ya Faɗi Wata Bukata

A ranar 4 ga watan Nuwamba, 2021, Kamfanin Mangal Industries ya rattaɓa hannun kan wata yarjejeniya da kamfanin China na gina katafaren kamfanin Siminti da zai rika samar da Tan miliyan uku duk shekara.

Ana sa ran za'a kammala aikin a shekarar 2024. A wata sanarwa, shugaban kamfanin masana'antun Mangal, Injiniya Fahad Mangal, ya ce aikin zai laƙume aƙalla dala miliyan $600m.

Yawan dukiyar da ya mallaka

Yawan dukiyar da Ɗahiru Mangal, ya mallaka, ana ƙiyasin ta kai kusan dala biliyan $2.2bn dai-dai da Naira Tiriliyan ɗaya a kuɗin Najeriya. Wannan Dukiya da Allah ya ba shi ta sanya shiga sahun 10 na Attajiran Najeriya.

A wani labarin na daban kuma Bayan Shan Kaye, Ɗan Uwan shugaba Buhari ya fice daga jam'iyyar APC

Ɗan uwan shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, watau Fatuhu Muhammadu, ya fice daga jam'iyyar APC.

Honorabul Fatuhu ya kasance ɗan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Daura, Mai'Adua da Sandamu a majalisar wakilai.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Jerin Abubuwa 6 da Qatar Ta Yi Na Haskaka Musulunci a Gasar Kofin Duniya 2022

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: