Yajin-aikin ASUU ya zaburar da Dalibi, ya koma neman na-kai maimakon zaman banza
- Abdussalam Mohammed Chindo wani dalibi ne da ASUU ta jawo karatunsa ya tsaya cak a Jami’a
- A maimakon ya cigaba da zama haka kurum, Chindo ya fara hada ‘Bleach’ yana saidawa a robobi
- Tun tuni kungiyar ASUU ta ke yajin-aiki saboda zargin Gwamnati ta saba alkawarun da aka yi masu
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Gombe - Wani matashi mai suna Abdussalam Mohammed Chindo yana cikin wadanda karatunsu ya tsaya a dalilin yajin-aikin malaman jami’a.
Malam Abdussalam Mohammed Chindo mutumin jihar Gombe ne wanda yake karatun ilmin Injiniya a jami’ar Ahmadu Bello a garin Zaria.
Ganin har yanzu ba a cin ma matsaya tsakanin kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya ba, sai Abdussalam Chindo ya nemawa kansa mafita.
Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter a ranar Litinin 20 ga watan Yuni 2022, ya fara hada sinadarin ‘Bleach’ mai fitar da kazanta.
A cewar Chindo ya koyi ilmin hada wannan sinadarin ne a makaranta, don haka ya fara wannan sana’a da za ta rika kawo masa abin kashewa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Bayan tuntuba da nazari a matsayin dalibin aji uku a sashen karantar ilmin Injiniyan sinadarai a jami’ar ABU Zaria, na fara taba kasuwanci.”
“Ina hada Bleach a dalilin yajin-aikin kungiyar ASUU. Ina amfani da abin da na koya a makaranta a zahiri. Ku yi mani ciniki; duk kwalba N350.”
- Abdussalam Mohammed Chindo
Yadda aka fara ThinkBig Bleach
Legit.ng Hausa ta zanta da matashin a ranar Talata, ya kuma tabbatar mata da cewa ya koyi wannan sana’a ne a wajen aikin SWEP a bara.
Chindo ya ce saboda karancin jari, sai ya fara da kwalabe 50 domin ganin yadda abin zai kankama.
Dalibin mai shekara 22 yake cewa daga baya ya fahimci za a iya amfani da leda wajen kulla sinadarin domin saidawa masu bukatar kadan.
Matsalar da wannan Bawan Allah zai iya fuskanta wajen aikinsa shi ne tsadar leda. Mutum yana bukatar kudi masu kauri kafin ya iya farawa.
Tanadi katin zabe
A bangare guda, ku na da labari, Sheikh Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto ya yi kira da babbar murya a kan mallakar katin zabe watau PVC.
Farfesa Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto ya yi amfani da shafinsa na Twitter a kwanakin baya, ya ankarar da jama'a kan muhimmancin zabe.
Asali: Legit.ng