Wutar Lantarki Ta Lantarke Wani Saurayi Har Lahira Yana Tsaka da Chajin Wayarsa iPhone
- Wutar Lantarki ta halaka wani matashin Saurayi dan shekara 18 a duniya yana cikin Chajin wayarsa a jihar Delta
- Rahoto ya nuna cewa Matashin ya jona wayarsa kan Chaji a tushen waya, ya kwanta bacci kuma ya ɗora iPhone ɗin a ƙirjinsa
- Lamarin ya faru da yammacin ranar Talata a ɗakin ƙawar mamansa, wacce ta ɗakko shi da nufin ya yi hutu a wurinta
Delta - Wani Matashin sauryai dan kimanin shekara 18, Chibuike Emmanuel, ya rasa rayuwarsa sanadin wutar lantarki a yankin Ozoro, ƙaramar hukumar Isoko North, jihar Delta.
Daily Trust ta rahoto cewa Wutar ta lantarke matashin ne da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Talata yayin da yake Chajin wayarsa iPhone 8 a tushen wayar lantarkin.
A cewar wata majiya ranar Laraba, ƙawar mahaifiyar matashin yaron ta kai rahoton abin da ya auku Ofishin Yan Sanda, wacce ta ɗakko Mamacin daga jihar Legas domin ya yi hutunsa a tare da su.
Yadda Wutar Lantarki ta halaka Saurayin
Rahoto ya nuna cewa Matashin ya kwanta a kan Siminti a gidan ƙawar mamansa dake kan hanyar Idheze kuma ya ɗora iPhone dinsa a kan ƙirjinsa bayan ya jona Chaji sannan ya yi bacci.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Majiyar ta ce:
"Yayin da yake cikin wannan yanayin ne Wutar ta Lantarke shi har lahira. An yi gaggawar kai shi Asibitin Okeleke amma likita ya tabbatar da rai ya yi halinsa."
"Yanzu haka an kai gawar Matashin yaron ɗakin aje gawarwaki mai zaman kansa dake yankin Ozoro."
Yayin da aka tuntuɓe shi, Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Delta, DSP Bright Edafe, ya tabbatar da faruwar lamarin ga hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN).
A wani labarin kuma Bayan ganawa da majalisar magabatan ƙasa, Buhari zai sa labule da shugabannin tsaro
Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zai tattauna da shugabannin hukumomin tsaron ƙasar nan ranar Talata mai zuwa.
A ranar Alhamis da muke ci, Shugaban ya gana da majalisar magabatan ƙasar nan da ta ƙunshi shuwagabannin Najeriya.
Asali: Legit.ng