Wata Sabuwa: Kwamishinoni biyu sun yi murabus daga mukaminsu a jihar Akwai Ibom
- Yayin da guguwar siyasar 2023 ke cigaba da kaɗawa, Mutum biyu daga majalisar kwamishinonin Akwa Ibom sun yi murabus
- Kwamishinan cigaban tattalin arziki da tashar jiragen ruwa, ya mika godiyarsa bisa damar aiki da gwamna Emmanuel ya ba shi
- A cewarsa ya ɗauki wannan matakin ne domin maida hankali kan shirinsa na shiga zaɓen gwamna a 2023
Akwa Ibom - Kwamishinan cigaban tattalin arziki da tashar jiragen ruwa na jihar Akwa Ibom, Mista Akan Okon, da kuma kwamishinan kwadugo, Fasto Sunday Ibuot, sun yi murabus daga mukamansu.
Wannan na ƙunshe ne a takardu mabanbanta da manema labarai suka samu da yammacin ranar Litinin a Uyo, babban birnin jihar, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Okon, a wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 14 ga Maris, 2022, ya ce ya ɗauki matakin murabus ne domin maida hankali kan kudirinsa na shiga zaben gwamna a 2023.
Wutar lantarki ta dauke a Legas, Abuja Kaduna da wasu jihohi gaba daya, kamfanonin lantarki sun bayyana
Ya kuma gode wa gwamna Udom Emmanuel bisa damar da ya ba shi kuma ya yi wa gwamnatinsa da jihar fatan kawo cigaba ga al'umma.
Mista Okon, ya ce:
"Yau Litinin 14 ga Watan Maris, 2022, na mika takardar murabus ɗina daga majalisar zartarwan jihar Akwa Ibom daga matsayin kwamishinan cigaban tattalin arziki da tashar jiragen ruwa."
"Babbar dama ce da gata na yin aiki wa jiharmu karkashin jagorancin Udom Emmanuel a bangare mai muhimmanci. Ina godiya ga Allah da mai girma gwamna bisa damar da na samu."
"Ina mika godiyata ga al'ummar jiha baki ɗaya bisa goyon bayansu da kara mun kwarin guiwa wajen sauke duk nauyin da aka dora mun."
Kwamishinan Kwadugo ya yi murabus
Kazalika, Kwamishinan kwadugo da tsare-tsare, Fasto Sunday Ibuot, a wata takarda mai taken, "Murabus daga mukami." ya gode wa gwamna tare da tabbatar masa ba zai taba mance wa da gatan da ya masa ba.
Punch ta rahoto ya ce:
"Cikin matukar girmama wa ina mika godiyata ga mai girma zababben gwamnan jihar Akwa Ibom bisa babbar damar da ya bani ta Honorabul Kwamishina a jihar mu. Wannan ba karamar dama bace."
"Da farko sakataren kwamitin fasahar noma da samar da abinci, daga baya na koma mashawarci na musamman kan harkokin siyasa/majalisa da albarkatun ruwa kuma daga karshe Kwamishinan Kwadugo."
"A tsawon wannan lokaci na yi iya bakin kokarina wajen sauke nauye-nauyen dake kaina. A yanzun ina mai murabus daga mukamina bisa wasu dalilai na ƙashin kaina."
A wani labarin na daban kuma Shugaban PDP ya yi magana kan gwamnan dake shirin ficewa ya koma jam'iyyar APC
Shugaban PDP na ƙasa ya kori duk wani raɗe-raɗin dake yawo cewa gwamnan Edo zai fice daga jam'iyyar ya koma APC.
Sanata Ayu ya ce ba inda gwamna Obaseki zai je, kuma PDP zata kafa kwamitin da zai magance saɓanin dake cikin PDP a jihar.
Asali: Legit.ng