Dan Shekara 21 Na Ke Son Aure: Yar Shekara 70 Da Bata Taba Aure Ba, Bata Taba Sanin Namiji Ba

Dan Shekara 21 Na Ke Son Aure: Yar Shekara 70 Da Bata Taba Aure Ba, Bata Taba Sanin Namiji Ba

  • Wata mata yar shekara 70 mai suna Genevieve ta bayyana cewa tana bukatan saurayi dan shekarar 21
  • Matar wacce ke da nakasar kafa bata taba fita daga gidanta ba kuma bata taba saurayi ba
  • Genevieve ta kwashe wadannan shekaru tana rayuwa cikin gida sakamakon cutar da ta hanata amfani da kafafunta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Wata mata yar shekara 70 mai suna Genevieve wacce bata taba aure ba ko saurayi ko sanin namjiji ba ta bayyana irin namijin da take so.

Genevieve na fama da nakasar kafa wanda ke hanata tafiya.

Bata taba saurayi ko makaranta ba

A hirar da tayi da Afrimax, matar ta bayyana cewa ba haka aka haife ta ba a shekarar 1952. Amma daga baya iyayen ta suka gani bata iya tafiya sai da rarrafe.

Kara karanta wannan

Muje zuwa: Wata mata ta hango alheri bayan da Dangote ya samu kishiya wajen gina matatar mai

Ana kyautata zaton cewa Genevieve ta kamu da cutar ne lokacin tana yarinya wanda ya nakasa kafafunta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakamakon haka iyayenta basu sa ta a makaranta ba saboda basu da kudin keken guragu kuma ba za su iya rika kai ta makaranta kullum ba.

Yar shekara 70 wacce bata taba aure ba
Yar shekara 70 da bata taba aure ba, bata taba sanin namiji ba ta ce dan shekara 21 ta ke so Hoto: Afrimax
Asali: UGC

Makwabtanta suka kai mata dauki

Bayan rasuwar iyayenta, makwabtanta suka kawo mata dauki suna kai mata abinci jefi-jefi.

Ta bayyanawa dan jaridan da ke hira da ita cewa tana bukatan saurayi dan shekara 21 matsayin masoyi kuma tana son aure.

Kalli bidiyon:

"Hada Turo IV": Matashi Ya Koka Bayan Budurwarsa Za Ta Auri Wani Daban, Hirar Su Ta Bayyana

A wani rahoton daban kun ji cewa wani matashi mai amfani da sunan @sadeeq_malo a Twitter, ya bayyana labarin yadda ya samu tangarɗa a soyayyarsa.

Kara karanta wannan

Wani mutum ya fadi kalaman da ya yi amfani da su wajen sace zuciyar matarsa a Twitter

Matashin ya bayyana cewa da shi da budurwarsa sun kwashe shekara uku suna soyayya, sannan sun shirya yin aure.

Sai dai, abubuwa sun kwaɓe musu lokacin da iyayen budurwar ta sa suka shirya haɗa ta aure da wani daban.

A cewar matashin budurwar ta sa ta gaya masa cewa ba ta da wani zaɓi wanda ya wuce ta bi abinda iyayenta suke so.

Ya bayyana cewa har yanzu tana son shi amma ba za ta iya bijirewa iyayenta ba. Ta roƙe shi da ya yafe mata ya ɗauka komai ba komai ba ne kawai ya ci gaba da rayuwarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164