Sabbin bayanai 4 game da Dangote da baku sani ba: Zai iya kashe N415m kullum na tsawon shekaru 40

Sabbin bayanai 4 game da Dangote da baku sani ba: Zai iya kashe N415m kullum na tsawon shekaru 40

A shekara ta 11 a jere, hamshakin attajirin nan na Najeriya, Aliko Dangote, ya ci gaba da rike kambin lamba daya a jerin masu tarin kudi a nahiyar Afirka ba tare da fashi ko tsallake ba.

Kamar yadda mujallar Forbes ta fitar a baya-bayan nan, karin 30% na farashin hannun jarin simintin Dangote wanda ya biyo bayan karuwar gine-ginen a Najeriya daga 'yan kasa da gwamnati ya ba da gudummawa ga karin dukiyarsa

Legit.ng a bincikenta, ta kawo muku wasu sabbin abubuwa guda 4 masu ban sha'awa game da hamshakin attajirin wanda a halin yanzu dukiyarsa ta kai dala biliyan 13.9.

Mai kudin Afrika, Aliko Dangote
Sabbin bayanai 4 game da Dangote da baku sani ba: Zai iya kashe N415m kullum na tsawon shekaru 40 | Hoto: businessday.ng

1. Zai iya kashe N415m kullum nan da shekaru 40 masu zuwa cikin kwanciyar hankali ba tare da yin wani aiki ba

Kara karanta wannan

2023: Zan kawar da karuwai idan nayi nasara a zabe, Dan takaran shugaban kasa yayi alkawari

Karuwar arzikin da Dangote ya samu ya sa attajirin zai iya kashe dala miliyan 1 (N415m) a kullum nan da shekaru 40 masu zuwa.

Kuma zai iya yin almubazzaranci ko jin dadin kudin ba tare da ya yi aikin katabus ba na tsawon shekaru 40 masu zuwa, inji wani lissafin da Business Insider ya nuna.

2. Ya kashe akalla Naira Biliyan 415 a tsawon shekaru a kan ayyukan agaji

Hamshakin dan kasuwa mai shekaru 64, haifaffen Kano, sanannen babban mai taimakon al’umma ne.

Business Insider ta ruwaito cewa ya sauya rayuwar da dama a fadin nahiyar Afrika a cikin tsare-tsare daban-daban na ayyukan alheri da ya kai ga kashe akalla dala biliyan daya (N415 biliyan).

Kashe kudinsa a ayyukan alheri da alama ba su durkusa dukiyarsa ba, sai dai ma karin da ya samu.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Malaman makarantun firamare a Abuja sun tsunduma yajin aiki

3. Dukiyar da ta hadiye jimlar GDP na sama da 15 na kasashen Afirka

Arzikin Dangote a halin yanzu ya haura akalla GDP na fiye da kasashe 15 a nahiyar Afirka a hade.

Ana kuma sa ran wannan zai fadada idan matatarsa ta mai da ake aiki akanta yanzu ta kammala.

Business Day ta nuna cewa Dangote ya fi wasu kasashen Afirka arziki, kamar Malawi, Somaliya, Burkina Faso, Laberiya, Burundi da dai sauransu.

4. Dukiyarsa ta dara ta attajiran Afirka jerin 2 da 3 a hade

Har ila yau, arzikin Dangote ya zarce dukiyoyin attajirai na biyu da na uku a Afirka.

Forbes ta saki rahoto kwanan nan cewa, Johann Rupert da dangin Afirka ta Kudu da Nicky Oppenheimer na kasar da aka ambata a Afirka sun zo na biyu da na uku bi da bi a jerin attajiran Afrika.

A wani labarin, a makon nan ne aka ji shugaban bankin cigaban Afrika, Dr. Akinwumi Adesina ya kai ziyara zuwa matatar Aliko Dangote da ake kokarin karasawa a garin Legas.

Kara karanta wannan

Kotu ta yankewa wasu masu walder 4 daurin shekaru 7 a kurkuku saboda satar N15m

Akinwumi Adesina ya yaba da wannan gagarumin aiki ma babban mai kudin Afrika. Mutane 38, 000 za su samu aiki, baya ga fetur da takin zamani da za a rika samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.