Matashi da kanwarsa sun bayyana yadda tsawo da girman jikinsu ya zamo musu matsala

Matashi da kanwarsa sun bayyana yadda tsawo da girman jikinsu ya zamo musu matsala

  • Wasu 'yan uwa biyu masu girman jiki sun zama abin tausayawa a intanet bayan mai yawon bude ido Joe Hattab ya gano su kuma ya yi bidiyon a kansu
  • Mohammed, da ya daga ciki ​​mai girman jiki, ya koka da yadda rashin abin dogaro da kai ya dame shi domin babu wanda yake son daukarsa aiki
  • Da take magana, mahaifiyarsu ta bayyana cewa ta haifi ’ya’yanta daidai amma sun fara sauyawar da ba za a iya kwatantawa ba tsakanin shekaru 12 zuwa 14

Alkahira, Masar - A baya-bayan nan an ga wasu mutane biyu mafi tsayi a duniya a wani gari mai suna Ash Sharqia da ke birnin Alkahira na kasar Masar.

Shahararren mai yawon bude ido Joe Hattab ne ya gano ’yan uwan biyu kuma sun ja hankalin masu amfani da intanet da tsawonsu mai ban tsoro.

Kara karanta wannan

Shehu Sani: 'Yan bindiga sun zama jiha mai zaman kanta a cikin jihohin Arewa maso Yamma

Kullum girma muke: Matashi mai girman jiki ya koka kan halin da yake ciki
Kullum girma muke: Matashi mai girman jiki ya koka kan halin da yake ciki | Hoto: an ciro hotunan daga bidiyon da Joe Hattab ya yada
Asali: Facebook

Kullum kara girma suke

Namijin mai suna Muhamed Shahat ya bayyana cewa an haife shi ne daidai da kowa amma ya fahimci yana saurin girma tun yana dan shekara 14.

Yanzu yana da shekaru 34, matashin ya kai tsawon mita 2.47, kusan rabin mita kenan kasa da mutumin da ya fi kowa tsayi a duniya wato Sultan Kösen wanda ke da tsawon mita 2.51.

Saboda girmansa da tsawonsa, Muhamed ya koka da yadda masu daukar ma’aikata suka ki daukarsa aiki, wanda hakan ya sanya shi rashin samun aikin yi.

Wani abin sha'awa shi ne, saurayin ya bayyana cewa har yanzu kara girma yake, haka nan 'yar uwarsa Huda da ke tsayin mita 2.40.

Mahifiyarsu na neman taimako

Da take tabbatar da furucin Muhamed, mahaifiyarsa ta bayyana wa Joe Hattab cewa ta haifi 'ya'yan nata kamar kowane yaro amma abin mamaki sun fara girma mara misaltuwa tun daga shekaru 12 da 14.

Kara karanta wannan

Benue: Ɗan shekaru 44 ya cire ƴaƴan marainansa da kansa don daƙile tsabar sha'awarsa

Ta koka kan yadda tsayin su ya hana su wasu abubuwa da dama kuma ta bukaci mutane su kawo agaji ga 'ya'yanta.

A cewarta, suna bukatar samun waraka don dakatar ci gaba da girman da suke yi cikin sauri.

Kallin bidiyonsu:

Mutane da yawa sun nemi taimako ga ’yan’uwan biyu

Ronnie Assimonye ya ce:

"Ina musu fatan su sami maganin yawan girman kwayar halittarsu. Wannan ita ce babbar matsalar. Idan ba haka ba, za su ci gaba da girma kuma su ci gaba da gajiya."

Yolly Docena-Saeed ya rubuta:

"Ya kamata gwamnatin Masar ta taimaka musu, a ba su abin da za su dogaro dashi domin su tsira, macen za ta iya aiki a gida kamar ta koya mata gajeren kwas kamar dinki, ko dai duk wani aikin da zai dace da kwarewarta da saukin koyo."

Najma Mohd Azam ya ce:

"Ya kamata kasarsu ta tsaya musu tsayin daka don sanya su a kudin tarihin Guinness ta hanyar ba su taimakon lafiya, taimakon tunani da kudi."

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wani gida, uwa da jaririnta sun kone a Kano

Imankhan Marvin Anwar Carlos ya ce:

"Zai iya yin nasara a WWF kamar Great Khali na WWF. Ko kuma ya buga wasan kwallon kwando. Abin da yake bukata shi ne abinci mai lafiya da horarwa mai kyau. Kuma bayan shekaru 2 na aiki tukuru zai iya sauyawa. Idan wani ya ba shi dama kuma idan a shirye yake."

A wani labarin, mutum mafi tsawo a tarihin duniya, Sultan Kosen ya nufi kasar Rasha don nemo matar aure wacce za ta haifa masa yara, The Guardian ta ruwaito.

A farkon watan Disamba Kosen ya tafi Moscow don neman matar aure. A cewarsa ya je Rasha ne saboda yadda ya ji labarin matan kasar su na da kyau da iya soyayya.

Hakan ya sa ya yanke shawarar amaryarsa ta kasance ‘yar kasar Rasha inda yake so ta haifa masa da namiji da diya mace, rahoon

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.